YADDA AKE CEWA INA ƘAUNARKI/KA CIKIN NISHAƊI


YADDA AKE FADAR INA KAUNARKI / KA CIKIN SHAUKI

Fadawa kogin soyayya abu ne mai sauki. Hakama Fada wa Masoyi ko masoyiya , ina son ka /ki, bai da wahala. Sai dai ya kan yiwa masoya wahala idan lokaci yai tsawo. Musamman ace kalmar ta dinga tasiri tamkar farkon soyayyarku ne. Kuma lalle akwai bukata yawan fadar Ina kaunarki / ka. Sai dai a tabbata da gaske ake. Kuma cikin hanyoyi daban-daban. Niyya da tasirin kalmomin shi ne muhimmi. Shi ke sanya bugawa zuciya. Ya sa shakuwa da Bege. Ya habaka soyayya ta dinga karuwa.

Muna so ace dukkan sanda ka fadi "Ina kaunarki / ka" Ta zama ta sanya farin ciki da harbawa zuciya, ga masoyi da ke sauraro. Saboda haka sai anbi wasu hanyoyi daban-daban. Cikin canja salo tare da 'yan dabaru. Ayyukanka na magana ga masoyiyarka, ba ma tare da furta kalma ba. Misali :

Wajen kwanaki 4 kenan , ina cikin bacin rai da damuwa. Ni kaina ba zan ce ga asalin matsalata ba. Ina zaune kan tabarma zuciyata cike da jin haushi Mai gidana. Na dora ruwa zan yi tuwon masara kenan. Sai na ji waya : kar ki dora tuwo yau , ki shirya bayan isha za ki rakani anguwa". Sai ya kashe wayarsa.
Duk da kasancewarsa talaka, amma yana da kokari akan gidansa. Sai dai kuma ba ya birge ni. 
Tunani na fada: Anguwa kuma? To ina za mu? Wani abu ne ya faru a gidansu Goggo? Nan da nan na canja kaya. Ina idar da sallar isha kuwa sai gashi. Yai ma na shata adaidaita ( Opay ). Bayan mun zauna na ce lafiya kuwa ? Ya ce kalau . Sai ya kamo hannuna ya dora akan cinyarsa. Kawai sai na ji wani sanyi araina. Ya na riqe da hannuna har muka isa Yahuza Suya. Ya biya adaidaita ta cikin waya. Mu ka sauka ya ce zo mana. Ya nuna min kujerun waje na dai-dai shuke-shuke. Shi kuma ya wuce wajen siyayya. Sai gashi da kaza da lemo ( ice cream ). Ya bude muna ci. Sai ya sa hannu a aljihunsa. Ya ce miko hannunki. Sai gashi ya dora min wata guntuwar takarda . Cikinta ya rubuta da kansa : INA KAUNARKI SOSAI, A MATA BABU IRINKI " Habawa sai na jawo hannunsa na dinga sumbata ba adadi. Na kara kurawa takardar nan ido ina rike da hannunsa gam. Har sai da na ji hawaye sun fara gangarowa a kumatuna. Kawai na mike na fada jikinshi. Sai ya ce ke : Mutane na kallonmu. Ni kuwa nai kamar ban ji ba. Bayan na gama juye-juye na ajikinsa. Na dago na ce: Wallahi na ji dadi sosai. Sai na ji nan da nan zuciyata ta cika makil da soyayyarka. Na gode kwarai. Muna gama wa kuwa ya zaro waya ya kara mana shata adaidaita. Muna shiga na kwanta jikinsa, ya riko ni har muka isa gida. 
Sai na killace takarda ta da kyau. Akodayaushe ganinta na tuno min da fitarmu. Kuma inji wani sabon farin ciki. Gaskiya da na dauka ma, mijina bai iya soyayya ba. Shiyasa sam ba ya birgeni acan baya.

To kunga Akwai ayyuka da dama da su ka wakilci "INA KAUNARKI SOSAI" A wannan labari. Wato yin furuci ➕Aiki = Soyayya Ingantacciyya. 

*HANYOYIN FADAR INA KAUNARKI / KA :*

*LOKUTA :* Masoya su dinga fadar ina kaunarki a lokuta daban-daban. 
1 -Da safe za'a rabu ( zai je aiki).
2 - Lokacin haduwa ( ya na shigowa gida). 
3- Lokacin da za ayi bacci .

*YARE :* Amfani da yare kala-kala wajen fadar Ina sonki. Larabci , da fulatanci , da Barbanci , da Yarbanci , da dai sauransu. 

Larabci : Uhibbuki 
Fulatanci : Mi yidi ma
Barbanci : Nya Raina
Yarbanci : mo nife re
Inyamuranci : a hurum gi n'anya .
Turanci : I love you

*WURARE :* Canja wurare daban-daban koyaushe. Ka fada a daki. Anjima ka same ta a madafa ( kitchen) . In za ka fita abakin kofa. In ka ajiye ta a unguwa.

*RUBUTU :* Rubuta kalmar ina kaunarki / ka. 
1 - A rubuta da rubutunka / ki a takarda ko wani kwali ( cardboard paper) a bawa Masoyiya/ yi.
2 - Tura ma masoya ta waya. A sakon kar ta kwana ( text message) .
3 - Katin soyayya ku siya ku bawa Masoyanku.

*HOTUNA :* Tura hoton filawa , zuciya , tsuntsaye mai jan hankali. Da mai hade da kalmomin soyayya. Ta cikin Hanyoyin yanar gizo ( email , Whatsapp, ...).

*KYAUTA :* Kyauta babbar alama ce ta soyayya. Ana son ba da kyauta daga lokaci zuwa lokaci. Misali : Turare , sutura, zobe , agogo , da dai sauransu.

A karshe dai dukkanin wadannan da ma suran irinsu. Ayyukane da ke fassara cewa :" Ina KAUNARKI / KA". Kunga daukarsu da muhimmanci. Da sabawa da yinsu acikin rayuwarmu zai dinga habaka soyayyarmu.

✍ *Amina Yusuf Gwamna*
Litattafai da aka duba:
1 - Islamic Education.
By Iqraa charitable society. Jeddah, Saudi Arabia.

2 - 101 Amazing ways to say "I love you ! ".
By Cucan Pemo.
Post a Comment (0)