DALIBAN ILMI KU FARGA
Kira da babbar murya gareku yan uwa daliban ilmi, Hakika malamai isharace gareku cewa akwai kalubale Mai girma agareku, ta yadda Idan malaman nan suka kare kune zaku gajesu, shin kun shiryawa zama kamar malaman ko sama dasu?? Kune zaku zama masu bada fatawa kune zaku zama fitilu na al'umma, Kun shiryawa zama hakan?? Ko kuma kuna so sai malaman Sun kare sannan ku farka daga baccin da kuke?? Lalle ya zama wajibi mu kara himma wajen neman ilmi mu tara abunda muka tara kafin su kare, Manzon Allah yake cewa acikin hadisin Abu Umama albahili cikin khudbar hajjatul wada'
" ﻳﺎ ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺧﺬﻭﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﻘﺒﺾ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﻭﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﺮﻓﻊ ﺍﻟﻌﻠﻢ "
Wanda kuma munsan cewa dauke ilmi shine mutuwar malamai kamar yadda Manzon Allah ya fassara acikin wannan hadisin.
Abdullah bin mas'ud yake cewa:-
« ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺑﺎﻟﻌﻠﻢ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﺮﻓﻊ، ﻭﺭﻓﻌﻪ ﻫﻼﻙ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ»
Abu darda'i yake cewa;
«ﻣﺎ ﻟﻲ ﺃﺭﻯ ﻋﻠﻤﺎﺀﻛﻢ ﻳﺬﻫﺒﻮﻥ، ﻭﺟﻬﺎﻟﻜﻢ ﻻ ﻳﺘﻌﻠﻤﻮﻥ، ﻓﺘﻌﻠﻤﻮﺍ ﻗﺒﻞ ﺃﻥ ﻳﺮﻓﻊ ﺍﻟﻌﻠﻢ، ﻓﺈﻥ ﺭﻓﻊ ﺍﻟﻌﻠﻢ ﺫﻫﺎﺏ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ »
Ya kai dan uwa kayi nazari sosai akan wannan magana ta sahabi Abu darda'i radiyallahu anhu ka dora daliban ilmin wannan zamani akanta da yawa daga cikin dalibai sun nesanta kansu daga malamai zaton su suma sun zama malamai sun koshi da ilmi hakan yasa suka dena nemansa, suka radawa kansu rawunan malanta suka Kai kansu matsayin da suna ganin sunfi kowa, «ﻭﺟﻬﺎﻟﻜﻢ ﻻ ﻳﺘﻌﻠﻤﻮﻥ»
Ya kai dan uwa dalibin ilmi ka zamanto mai Lizimtan malamai kada ka bari dan abunda ka sani ya rudeka, kayi amfani da damarka kafin malaman su kare kayi kokari ka kasance cikin wadanda Allah zai shiryar da al'umma adalilinsu, kada ka kasance cikin wadanda Manzon Allah ya siffanta mana su cikin hadisin Abdullah bin Amru bin Aas
«ﺣﺘﻰ ﺇﺫﺍ ﻟﻢ ﻳﺒﻖ ﻋﺎﻟﻤﺎ ﺍﺗﺨﺬ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺭﺅﻭﺳﺎ ﺟﻬﺎﻻ، ﻓﺴﺌﻠﻮﺍ ﻓﺄﻓﺘﻮﺍ ﺑﻐﻴﺮ ﻋﻠﻢ ﻓﻀﻠﻮﺍ ﻭﺃﺿﻠﻮﺍ»
Allah madaukakin sarki yasa mu kasance cikin wadanda zasu zamo fitila ga al'umma ba wadanda zasu batar da al'umma da jahilci ba. Ya Allah malaman da muka rasa kaji kansu kasa aljannah ce makomarsu Mukuma ka kyautata namu karshen.
# Zaurenfisabilillah