ANNOBAR GARIN BAGADAZA A SHEKARAR
1831AD/1246AH (Makamanciyar Covid 19. Amma
fa sawun Giwa ya take na Rakumi)
Dr. Magaji Falalu Zarewa
3 ga Sha'aban 1441H (28/03/2020)
Wannan annoba da ta faru a garin Bagadaza ta
canza komai daga muhallinsa, sai da ta mayar da
garin Bagadaza tamkar leda a cikin guguwa.
Ana iya cewa wannan Annoba ita ce Annoba mafi
firgici da tarihin duniya ya gamu da ita. Wadanda
Allah ya yi wa tsawon rai suka tsira daga wannan
annobar sun jima suna ba da labarin irin barnar da
ta yi.
A yanzu haka akwai wata kasuwa a garin Bagadaza
da ake kiran ta Ja’ifa (kasuwar mussa), dalilin kiran
ta da wannan suna, shi ne cikar da tayi fal da
gawarwaki lokacin wannan annobar, inda ba abin da
ke tashi sai warin gawa.
Wannan annoba ta fito ne daga arewancin
Bagadaza, a watan Yuli na 1830AD, gabanin isowar
ta Bagadaza mutanen garin sun samu labarin bullar
ta a garin Tibriz na Iran. Bayan wata biyu kuma sai
ga labarin bullarta a garin Karkuk.
*TSARIN KILLACE MUTANE (Quarantine)*
Jin haka ke da wuya sai sarkin Bagadaza Dawud
Basha ya nemi babban likitan ofishin jakadancin
kasar Burtaniya da ya fitar da tsarin Quarantine,
(killace mutane don tsaron lafiyarsu) don dakile
isowar cutar zuwa kasarsa ta Bagadaza, sai kuwa
likitan ya aiwatar da wannan tsari na Quarantine, da
kulle iyakokin kasar.
*MALAMAI SUN YI WA WANNAN TSARI BORE*
Malamai masu fatawa na kasar a wancan lokaci sai
suka bijire, da zummar cewa hakan ya saba wa
Shari’ar Musulunci, suka hana Sarki Dawud Basha
daukar duk wani mataki da zai dakile isowar
Annobar. Hakan kuwa ya ba wa fatake daga Iran, da
Kurdistan shigowa Bagdaza cikin kwanciyar hankali.
*MAI AFKUWA TA AFKU*
A cikin watan Maris na shekarar 1831AD, sai aka
samu mutum na farko da ya kamu da Annobar a
garin Bagadaza, a yankin da yahudawa ke zaune
masu kazanta, daga nan sai annobar ta ci gaba da
yaduwa a wasu yankuna.
Wani mazaunin garin a wannan lokacin mai suna:
Sulaiman Fa’iq ya ce: adadin gawarwakin da aka
fitar zuwa bayan gari a karshen watan Maris din sun
kai 1000. Zuwa tsakiyar watan Afrilu kuwa sai da ya
zama ana fitar da gawa kusan 3,000 a kowace
rana. Daga bisani, su kansu ma’aikatan da ke
rubuta adadin mamatan sai da ya zanto ba sauran
ko daya.
*TURAWA SUN DAUKI MATSAYA (IYA RUWA FID-DA
KAI)*
Ganin haka ke da wuya sai turawa da kiristocin da
ke da alaka da su, suka yi maza suka killace kansu
a gidajen su, bayan sun tanadi kayan masarufi, ya
zama ba su fitowa ko nan da can, ba su cakuduwa
da juna. In ma akwai abin da suke so daga waje
sai dai su janyo shi da igiya, ko wasu abubuwa
masu kama da filaya, sannan sai suyi masa hayaki
don kashe kwayoyin cutar da ke tare da shi, kafin
su yi anfani da shi. Hakan ta sa ba a samu
wadanda suka kamu da Annobar ba a cikin su da
yawa, wadanda ma suka kamu, sun harbu ne ta
hanyar maguna da suke shiga wurinsu.
*YANAYIN DA AKE CIKI GAME DA SAURAN
MAZAUNA GARIN*
Su kuwa sauran mazauna garin sai suka mika wuya
suka ce sun sallamawa kaddara. Annoba kuwa ta
rinka girbe su tana yi masu matsanancin kisa, har
sai da ta kai kimanin mutum 9,000 na mutuwa
kullum.
Duk da cewa wasu ma ba Annobar ce ta kashe su
ba, masifar shiga firgici ne ya kashe su.
*LABARIN WANI DAN MISHAN*
Akwai wani dan mishan mai suna Groves dan kasar
Burtaniya, wanda yake zaune a wancan lokacin a
Bagadaza. Daman ya bude wata makaranta ta
kiristoci marayu. A lokacin da wannan annoba ta
bullo, sai shugaban ofishin jakadancin kasar
Burtaniya ya ce ya kwashe yaransa su koma can
kauyukan Basra don gudun kamuwa da Annobar, sai
Groves ya ki, ya ce ya dogara ga Allah. Sai ya kulle
gidansa shi ma, da kimanin mutuane 12 a ciki. Ya
ce: daga gidan su akwai inda suke zama suna
hango abinda ke faruwa a waje, sai da ta kai ana
fitar da gawawwaki kimanin 17,000, a kowace rana.
*YANAYIN CIKIN GARI DA TITUNAN BAGADAZA A
WANNAN LOKACIN*
Groves wanda ya wallafa littafi kan wannan annoba,
ya ce: ta kai ba kowa a tituna face masu aikin fitar
da gawawwaki, da masu kawo ruwa don wanke su.
Sai da ta kai an rasa inda za a rufe gawa sai a
gafen tituna, har ma a kan hanyoyi, da duk inda aka
dan hangi fili, saboda cushewar da garin ya yi da
kayayyaki da kuma gawawwaki.
Ya ce: har sai da ya zama mutane sun saba da
mutuwa, ta yadda mutum dan uwansa zai mutu, zai
binne shi ba tare da wata damuwa ba.
Daga nan fa lamari ya kara kamari har ya kai
mutane na yanke jiki su fadi a kan tituna su kadai,
ba wanda zai iya binne su, sai dai karnuka su zo su
ci abin da za su ci kawai, wasu ma lokacin rai bai
gama fita daga jikinsu ba.
Abin da ya fi komai tashin hankali a lokacin su ne
kananan yara da suke ta faman kuka bayan mutuwar
iyayensu mata. Baka iya rabe kukan na su da
haushin karnuka.
Groves ya ce: Abin da ya fi bashi mamaki, shi ne
yadda mutanen Bagadaza suka matsanta wurin
wanke gawa kafin a rufe ta, a cikin wannan yanayi,
alhali kuma kafin haka ba su damu da keta alfarmar
Allah ba.
Sai da komai ya yi tashin gwauron zabi har da
likkafani.
*YADDA TA KAYA DAGA KARSHE:*
Sulaiman Fa’iq ya ce: Sa ya ga abin ya fara kazanta,
tun lokacin ma, mutanen da suke mutuwa ba su fi
600 zuwa 700 ba a rana, sai ya je ya nemi izinin
mahaifinsa, wanda bafaden Sarki ne, cewa ya
kamata su fita su bar garin don tsira da rayuwarsu,
sai babansa ya ce, ya kai dana ai ba ya halasta a
guje wa Annoba. Duk wadanda suka mutu ta
sanadiyyar guduwarsu sun yi sabo, don haka mu yi
zaman mu, in ma mun mutu mun yi shahada, wanda
kuma ya tsira ya more.
Sulaiman ya yi kokarin gamsar da mahaifinsa yana
mai kafa masa hujja da cewa asalin wannan
kuskuren na maluman da suka ki ba wa Sarki goyon
bayan killace garin ne tun asali, kuma kai kasan
ra’ayinsu ne kawai ba na Shari’a ba. Mahaifinsa ya
gamsu, amma sai yace, duk da haka ba zai yiwu in
fita in bar Sarki Dawud Basha ba. Don haka ka tafi
kawai, ya bar ni, da in je in rayu takobin yan siyasa
ya kashe ni, gara in mutu ta wannan hanyar.
Sulaiman ya je ya debi yan gidansu ya fice da su
can nesa da gari, ya zama duk bayan kwana 4 sai
ya canza wuri, har dai Allah ya tseratar da su, babu
wanda ya mutu a cikin su sai wadanda ke shiga
cikin gari don nemo dan tsakin da za a sha.
Bayan Annobar ta lafa, sai Sulaiman ya yi maza ya
shirya komawa gida, musamman saboda barayin da
suke kusa da inda suke zaune, suke yi wa mutane
kwace.
Ya ce: Tun da suka fito ba su hadu da ko da
mutum daya ba a hanyar tasu, har sai da suka kai
gidajen kiristoci, sai ga wata mata ta leko, da ta
gan su, sai ta koma ciki ta kira yan uwanta cewa su
zo su ga wasu mutane a raye. Sai Sulaiman ya
tambaye ta yadda aka yi suka tsira, tare da cewa
babu ko da mutum daya da suka hadu da shi a kan
hanya? Sai tace: Ai tun lokacin da Annobar ta fara
yaduwa muka killace kanmu, kimanin mu 41, yanzu
mun zama mu 43, don an haifa mana yara 2,
kasancewar mun manta rabon da mu ga wani dan
Adam ya gitta, ganin ku ya sa muka yi farin ciki,
saboda hakan na nuna cewa Annobar ta tafi.
Ko da Sulaiman da jama'arsa suka isa gidansu, sai
ya garzaya fada, ya samu Sarki Dawuda Basha a
killace, amma yana kwance ba lafiya, ya kamu da
Annobar shi ma. Bayan yan kwanaki sai ya samu
sauki, a cikin wannan halin bayan samun saukinsa
ya ci gaba da kokarin lura da sha’anin mulki, duk
da raunin jikinsa, ya sa a ka nemo ma’aikata da za
su yi aikin kwashe gawawwaki yana biyan su kudi.
A lokacin kuwa ko ina cike yake da gawa; gidaje,
masallatai, kasuwanni, da hanyoyi.
Sai ya sa 'yan doka su yi ta aikin tsaftace garin, aka
sa lada akan kowacce gawa in mutum ya dauke, sai
aka rinka kwashe su ana jefa su kogin Dijla (Tigris
River) babu maganar wanka balle likkafani saboda
yawan su.
Mafi yawan gawawwakin ana daure kafarsu ne a
jikin bindin dabbobin da ba a san masu su ba sai a
kada su zuwa kogin suna jan gawar har cikin kogin.
Wannan tarihi mun dauko maku shi ne daga littafin
"Lamahátun Ijtima’iyyah min tarikh al-Iraq al-Hadith"
na Dr. Ali al-Wardi (1/269-275).
*YA ALLAH MUN TUBA KA YI MANA MAFITA DAGA
WANNAN HALI*
*ALLAH KA RABA MU DA KUSKUREN FATAWA,
MUSAMMAN WADDA KE DA ALAKA DA RAYUWAR
BAYINKA, DA HAKKOKIN SU.*