TAMBAYA TA 036


*013 AMSOSHIN TAMBAYOYINKU*

*YADDA AKE YIN WANKAN JANABA*

TAMBAYA:
Assalamu alaikum. Ina da tambaya, yaya ake wanka bayan an gama al'ada da kuma na janaba?
.

AMSA:

Wa'alaikumus salamu wa rahmatullah. Wankan janaba da wankan haila iri ɗaya ne, wato duka wankan tsarki ne, abin da ke bambanta su shi ne niyya. Wankan tsarki yana da siffofi guda biyu kamar yadda malamai suka koyar a littattafan Fiqhu, wato akwai Siffatul Ijza'i ( ﺻﻔﺔ ﺍﻹﺟﺰﺍﺀ ), akwai kuma Siffatul Kamal ( ﺻﻔﺔ ﺍﻟﻜﻤﺎﻝ ) . Ga bayanin yadda kowanne yake:


1. Siffatul Ijza'i ( ﺻﻔﺔ ﺍﻹﺟﺰﺍﺀ ): Wannan siffar wankan tsarki ne da bayan mutum ya qulla niyyar yin wankan a zuciyarsa, sai ya yi Bismillah, sai ya ɗibi ruwa ya game duk jikinsa da shi. Shi kenan ya gama wanka, sai dai wajibi ne ya tabbatar ruwan ya game ko'ina a jikinsa. Idan mai janaba ko mai haila suka yi wannan ya isar masu.


2. Siffatul Kamal ( ﺻﻔﺔ ﺍﻟﻜﻤﺎﻝ ): Wannan siffa ta wankan tsarki ta sha bamban da waccan ta farkon, ga yadda take; bayan mutum ya qulla niyya a zuciyarsa, sai ya yi Bismillah, daga nan sai ya wanke hannayensa sau uku kafin ya shigar da su cikin abin ruwa, daga nan sai ya wanke gabansa da duk inda qazanta ta taɓa, daga nan sai ya yi alwala irin alwalar sallah ba tare da wanke qafafuwa ba, bayan nan sai ya ɗibi ruwa ya zuba a kansa sau uku, daga nan sai ya wanke ɓarin jikinsa na dama daga sama zuwa qasa, bayan nan sai ya wanke ɓarin jikinsa na hagu daga sama zuwa qasa, bayan wannan sai ya wanke qafafunsa. Wannan ita ce siffar wankan tsarki ta kamala.


Wato duk wanda aka yi a matsayin wankan tsarki wanka yainganta, sai dai ta biyun ta fi kamala.


Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*
5/5/1440 h.
11/01/2019 m.
.

*👨‍👩‍👦‍👦Irshadul Ummah WhatsApp.*
*+2348166650256.*
Post a Comment (0)