BIJIREWA AIKATA WATA SUNNAH KAN IYA JAWO MAKA TABEWA.
Sahabi Abubakar Siddeeq Allah ya kara yarda dashi yana cewa "Ban kasance Mai barin wani abuba cikin abubuwan da Manzon Allah ya aikata ba face nima na aikatashi, ina tsoron kada inbar wani abu da ya aikata ban aikatashi ba in bata".
البخاري ٢٥٦
Al-Imam Ibnu Baddah Allah ya masa rahama yake cewa "Yaku yan uwana wannan fa (الصدّيق الأكبر) kenan yana tsoratawa kansa bata idan ya sabawa wani abu daga cikin umarnin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama.
Me kake tinanin zai faru ga zamanin da mutanen cikinsa suka wayi gari suna izgilanci da Annabin kansa, da kuma umarninsa, suke gasa wurin saba masa, suna wulakanta sunnarsa??
Muna rokon Allah kariya daga bata, da kuma tsira daga munanan aiki".
الإبانة الكبرى ١/٢٤٥
# Zaurenfisabilillah
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah