CIYAR DA ABINCI SALLAN DARE YANA SANYA KA A CAN SAMAN ALJANNAH...
عن أبي مالك الأشعري قال قال رسول الله صلى الله عليه وسلم إن في الجنة غرفة يرى ظاهرها من باطنها، وباطنها من ظاهرها أعدهاالله لمن أطعم الطعام، وأﻻن الكلام، وتابع الصيام و صلى والناس نيام
Daga Malik Al-Ash'ariy (R) ya ce Manzon Allah (saw) ya ce, Lallai a cikin Aljannah akwai wani bene ana ganin wajen sa daga cikin sa, kuma ana ganin cikin sa daga wajen sa, Allah ya tanade shi ga, wanda yake ciyar da abinci, kuma ya tausasa magana, kuma ya bibiyi Azumi, kuma ya yi sallah a halin da mutane suna bacci.
Imam Ahmad ya ruwaito kuma Albaniy ya ingantashi (Dariqus-salihin 61 pg)
Note:
•Komai na cikin Aljannah mai kyau ne, abinda kuma zuciya zata so ne, kai daga jin kwatance wancan kyakkyawan guri kasan ba karamin matsayin bane.
•Ciyarwa, wanda yake tunawa da wad'anda basu ci ba ya ciyar dasu
•Tausasa magana, shine mutumin da yake wa mutane kyakkyawan magana (magana mai dadi) misali magana ta kwantar da hankali idan kaga Dan uwan ka cikin tashin hankali.Gaishe da Dan uwan ka, yi masa godiya, fada masa kalmomi masu dadi, wanda baza su bata masa rai ba, domin Allah baya son masu munana magana wanda daka zauna dasu se sun baka damuwa saboda bakinsu baya fadin kyakkyawan magana.
•Bibiyan Azumi, ya zamana ka dauki wani Azumi da kake yawan yi, misali ka dau Azumin Annabi Dawoud yau Ka yi Azumi gobe kaci abinci..ko Azumin litinin da Alhamis, ko na tsakiya wata, 13,14,15..
•Sallah a lokacin da mutane suke bacci, tsayuwan dare (qiyamul-laili) hakan yana 'kayatar da Allah mai girma, ga mutane suna bacci, amma kai Ka tashi kanata neman kusanshi gare shi Subhanahu.
•Wasu malamai suka ce baza ka samu wancan katafaren matsayi ba cikin Aljannah se ka had'a wad'an can kyawawan ayyuka guda hud'u (4)
Wasu kuma suka ce a'a ko wani ka samu cikin wad'an acan ababe kana aikatawa zaka dace da wannan falalar, wanda shine abinda yafi inganci.
Allah Ta'ala ya bamu ikon Aikatawa, tare da kyakkyawan niya, ya jik'an iyayen mu ya temaki yan uwan mu da malaman mu.da dukkan musulmai gaba d'aya.
ZaurenFisabilillah
18/5/2019
https://t.me/Fisabilillaaah