BURGE MUTANE BA NAKA BANE


BURGE MUTANE BA NAKA BANE, BA ABUNDA ZASU AMFANA MA

Muhammad bin Aslam Allah ya masa rahama yake cewa "Na kasance akashin bayan mahaifina ni kadai, sannan na dawo cikin mahaifiyata ni kadai, sannan na fito duniya ni kadai, sannan za'a karbi raina ni kadai, sannan a shigar dani cikin kabarina ni kadai, sannan munkar da nakeer suzo su tambayeni ni kadai, idan nasamu alkhairi na samu ne ni kadai, sannan a dora min ayyukana da zunubaina akan mizani ni kadai, idan aka turani zuwa aljannah in tafi ni kadai, idan ma wuta aka turani ni kadai zan tafi, TO MEYE HADINA DA MUTANE?? 

صفة الصفوة ٤/١٢٦

# Zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)