HAƘIƘANIN RAYUWA MAI DAƊI


HAƘIKƘANI RAYUWA MAI DADI. 

Shaikh Ibnu Uthaimeen Allah ya masa rahama yana cewa "Rayuwa Mai dadi da nagarta ba ita bace yadda dayawa daga cikin mutane ke fahimta ba, cewa; kubuta daga kowane bala'i na daga talauci, da cututtuka da damuwa ba,  
     Sai dai Rayuwa Mai dadi nagartacciya shine mutum ya kasance Mai zuciya Mai kyau, Mai yalwataccen kirji, Mai yarda da abunda Allah ya hukunta ya kuma kaddara masa, idan alkhairi ya same shi ya godewa Allah, hakan Karin alkhairine agareshi, idan kuma abu na cutarwa/sharri ya same shi sai yayi hakuri, hakan ma alkhairine agareshi, wannan shine rayuwa mai dadi, kuma shine samun nutsuwar zuciya. 
     Amma tarin dukiya da lafiyar gangan ciki zata iya kasancewa halaka da sanadiyar tabewan mutum. 

فتاوى إسلامية ٤/٦٤

# Zaurenfisabilillah
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)