CORONAVIRUS: JARUMI SHAH RUKH KHAN YA TALLAFAWA ƘASAR INDIA


CORONAVIRUS - JARUMI SHAHRUKH KHAN YA TALLAFAWA KASAR INDIA

A yayin da cutar covid 19 wato coronavirus ta mamaye kasahen duniya India ma bata tsira ba. A saboda haka ne masu kudi, celebrities suke ta bada tallafi da gudummawa domin taimakawa gwamnati wajan ganin an yaki cutar.. Celebrities daga Bollywood da dama sun bada gudummawar su. Yayin da labarai ya dinga yawo a kafafen labarai cewa jarumi Srk yayi biris yaki bada nasa Donation din, se ka gashi yayi kukan kura yayi wuf yazo da wani irin salo wanda wannan ya wuce Donation se dai ace taimako gagarumi da karade gurare da yawan gaske

Taimako ne da suka kai mataki wajan bakwai zuwa takwas kamar haka 

Da farko dai akwai Donation da aka bayar a gidauniyar PM cares da prime minister Narendra Modi ya Kafa don taimakawa wadanda larura irin wannan ta afka masu

A mataki na biyu an kuma bada gudummawa ga gidauniyar Maharashtra CM relief fund

A mataki na uku Shahrukh khan yace wajibi a baiwa ma'aikatan lafiya kwarin gwiwa da kulawa ta musamman a wannan yanayin sabo da su ne jaruman a yanzu, sune suke saka tasu rayuwar a hatsari don ganin sun ceto rayuwar mutane da dama. A saboda haka zaa basu gudummawa ta personal protective equipments kits (PPE kits) kimanin guda dubu hamsin ga su ma'aikatan lafiyan.

Personal protective equipments kit akwatu ne da yake zuwa da kaya da likitoci ko ma'aikatan lafiya ke sakawa dan samun kariya daga daukar cuta mai saurin yaduwa a lokacin da suke treatment na mara lafiya.. Kayan sun kunshi hand gloves, gowns, face masks, da sauran su

A mataki na hudu, ta hanyar gidauniyar sa Meer foundation zaa samar da abinci a kullum ga iyalai guda dubu biyar da dari biyar (5500) akalla na tsawon wata daya, a birnin Mumbai

A mataki na biyar zaa samar da kitchen wanda zaa dinga girka lafiyayyun abinci kimanin guda dubu biyu (2000) a kullum domin taimakawa gidaje da asibitocin da bukatun su abinci baya isar su a rana

Bacin haka za a samar da abinci da darajar sa a kudi ya kai 3 lakhs ga marasa karfi da kuma kananan ma'aikata guda dubu goma a kullum

Sannan za a samar da abubuwan amfani na yau da kullum wanda suka danganci abinci, kayan miya, da sauran su wato grocery items ga kananan ma'aikata fiye da dubu biyu da dari biyar (2500) har na tsawon wata guda a garin Delhi.

Bai de gajiya ba still zai sa a dau nauyin biyan monthly allowance ga victims na acid attack kimanin mutane dari a garuruwan UP, Bihar, Delhi, west Bengal da Uttarakhand

Idan aka yi rough estimate na kudaden da zaa kashe zai zama kamar haka

PPE KITS - duk kit daya ana samun sa within 2000-4000 rupees. Akwai sources da suka tabbatar cewa PPE KITS din guda dubu hamsin zasu kama 23cr 

Abincin da zaa dau nauyin ciyar da families guda 5500 zai lashe kudi kimanin 7-10cr

Groceries da zaa dinga bawa kullum har na tsawon wata daya ya kama kimanin 2cr.

Abincin da zaa dinga girkawa guda dubu biyu wanda aka hada kitchen musamman domin sa ze ci kimanin 2cr.

3 lakh meal kits da zaa zaa kananan ma'aikata da masu kananan karfi kimanin mutane dubu goma zai kama wajan 20cr 

A takaice, rough estimate na hidimar da za a yi zai kama wajajen 50-54cr 

Se dai Srk bai bayyana ainihin abinda ya sanya a Donation na PM relief fund ba, wannan ya faru ne sbd tsarin sa na boye taimako da aka san shi da shi tuni.. Se de a yau wani tsohon dan jarida mai suna S Ramachandran a shafin sa na Twitter ya tabbatar da cewa gudummawar da Srk ya bayar ta kai kimanin 70cr. Amma a cewar sa, Srk din yayi shiru daga fadin haka.. Ga abinda ya rubuta

Sources: #ShahRukhKhan has donated over Rs 70 crore in kind to fight #COVID19India
But his lips are sealed on the amount!

If sources are to be believed, to gudummawar da ta fita a sandiyyar Srk ya haura 120cr, wanda ba ma se na fada ba, kowa ya san 120cr budget ne na manyan fina finai a Bollywood.

A lissafi na kudin Nigeria, kudin ya kama sama da naira Biliyan shida (over 6 billion naira) 

Sannan a yau da safe labari ya kara fitowa cewa Srk ya bada personal office nasa mai bene hawa hudu domin ayi amfani da shi wajan killace mutane (quarantine).

Lallai ba a banza ba a banza aka kira shi King of charity ba

AKK
Post a Comment (0)