*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*
*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 06🍍🍊*
*(Fitowa ta Shida)*
*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*
Idan har mun yarda da maganganun masu ilimin kimiyya da cewa gaskiya ne, to zai yi kyau kuma mu ga me likitoci suka ce dangane da azumi, masamman dogon azumi wanda zai dauki tsawon kwanaki ana bugawa, kamar dai Ramadan ko na watan Hajji wanda akan kwashe kwana 9 ana yi, kamar yadda muka kawo ne a matsayin shimfida, zai yi kyau kuma mu warware zancen dalla-dalla tare da neman Allah SW ya datar da mu.
1) Bincike ya nuna cewa azumi yana taimakawa wajen rage gurbataccen sinadarin da ake samu a cikin abinci, domin duk abincin da mutum zai ci akwai sauran da jiki ba ya iya dauka, wanda nan da nan yake juyawa ya zama poison a cikin jikin mutum, mafi yawancin wannan rubabben sinadarin yakan maqale ne a cikin kitsen da ke jiki, to a lokacin azumi wannan kitsen yakan qone kakaf, masamman a azumi mai tsawo.
Hakan kuwa yakan faru ne tare da taimakawar hanta, qoda da sauran da suke yin irin wannan aikin.
2) Azumi yakan taimaka kuma wajen hutar da kayan ciki, sai dai natural physiology ya ci gaba da ayyukansa, masamman wajen fito da ruwan sinadarin da yake taimakawa wajen narka abinci, amma daidai gwargwado, irin wannan aiki a sanadiyyar azumi zai sa daidaituwan ruwayen cikin jiki, duk da haka akwai buqatar masu gyambon ciki su kusanci likitoci domin jin shawarwarin yadda za su gudanar da rayuwarsu a watan azumi.
3) Cututtuka masu alaqa da radadi na cikin gabubba sukan ragu kadan.
4) Haka kuma azumi yakan taimaka wajen sauke hauhawar mizanin sukari, yadda yake karya qaruwar sinadarin Gulukoz, ya qara wa jiki kuzari, ta yadda zai rage yawan Insolin, almuhin azumi yana rage yawan Glucose a cikin jini.
5) Azumi yakan taimaka wajen qara narka kitsen dake cikin jiki, ta wajen rage yawan Gulukoz, wanda zai ba kitse daman narkewa don kuzari ya sami gindin zama, masamman ma kitsen da yake tattare a qodar mutum da gabubuwansa.
6) Azumi yana da amfani ba qarami ba ga masu hawan jini, yana daya daga cikin hanyoyi na al'ada da ake bi don sauke hauhawan jini, koda yake turawa ba za su ce mutum ya yi azumi ba, amma za su umurce shi da qaranta abinci don samun sauqin shawo matsalar.
Azumi yakan taimaka qwarai wajen rage yuwuwar kamuwa da cutar Arteriosclerosis, ko mu ce daskarewar kitse a cikin hanyoyin jini, a watan azumi kitsen yakan qone, glucose din kuma ya kakkatse, da haka ne sai ka samu ko mai hawan jini ne mizanin yakan sauko qasa.
7) Azumi yakan rage qiba mai cutarwa, da yadda yake hana taruwar kitse a cikin jiki.
8) Azumi yakan kwadaitar da mutum son cin abinci na al'ada, duk qwalamar mutum ga toye-toye yakan ragu, wani ma yakan bari gaba daya, in ma ya yi to da rana ne, da zarar ya sha ruwa sai ka ga ya fi son 'ya'yayen bishiya, da sauran nau'o'in abinci wadan da suke qara lafiya a cikin jiki, masamman ruwa da ababan marmari irin 'ya'yayen bishiyan.
9) Ba iyakansa kenan ba, yana dada qara qarfin garkuwar jiki, sabo da kawar da gurbataccen sinadarin dake jiki wanda ya samu ta hanyar abinci, ya saukar da yawaitar taruwar kitse a jiki.
Lokacin yin bude baki, a lokacin da aka ci 'ya'yan bishiya akan sami qaruwar vitamins kamar dai A da E wadan da suke taimakawa wajen korar CO2, wannan zai sa garkuwar jiki ta yi qarfi.
10) Azumi kan taimaka wajen rage shaye-shaye da duk abubuwan da suke da nekotin da kafé da sauransu, a wadannan abubuwa za mu iya gane dalilan da suka sa aka wajabta mana yin azumi, zai yi kyau mu fahimci cewa yin azumin shi ne ya fi mana sama da shan ruwa ko cin abinci ko jima'i, sai dai duk da haka marasa lafiya kamar olsa, sikila, ciki da shayarwa da sauran cututtuka yana da kyau su ga likita, su tattauna matsalolinsu da shi.
*Gabatarwa: Zauren Sunnah*
*Gamasu Sha'awar Bibiyar Karatukanmu Akan Shafukan Sada Zumunta Kamar WhatsApp da Facebook Zasu iya Bibiyarmu ta Wannan Hanyar*
*_Sai kuturo da Cikakkiyar Sallama. Da Cikakken Suna Tare da Adreshi ta Wadan nan Numbobin_*
_*WhatsApp Number*_
+2348039103800.
+2347065569254
_*Facebook @Zauren Sunnah*_
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/
*اللهم لا تواخذنى بما نقولوا واجعلنى خيرا مما نظنون. فقلت ما قلت. إن تك حسنة فمن الله وإن تك سيئة فمن نفسك والشيطان. وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت. وأستغفر الله
لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرو الوبركاته
*والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته*