TATTALIN KAYAN MIJI


*💕SHALELE CE 💕*
    08080702182

    *FREE SEMINAR*

  ABINDA AURE YA KUNSA 

24.TATTALIN KAYAN MIJI ; Aduk lokacin da namiji ya zabeki amatsayin mtrsa kisani fa nauyi yahau kanki hakkine ne akan ki ki kula ki tattala mishi dukiyarsa ,tunda yadauki yarda yabaki ya saka kudi yagina gida yasakaki ciki tofa kisani duk abinda gidan ke dauke dashi dama shikansa mijin yazama mallakinki dole kibasu kulawa , Amma anan inata magana akan tattali barin fayyace muku wani irin tattali nake magana akai agaskiya abune mayuwaci kasamu matar auren datayi haihuwa fiyeda daya wae kayan amfaninta suna Nan da tsaftrsu Basu kokkode ba gaskiya Koda su maza suna matse hannu akwae sakacinmu Mata wata tun daga pentin gidanta Zaki tausayawa mijinta akwae namijin Dana sani meson tsaftr tsiya Amma saboda kazantr matarsa duk wata 3 se ansake penti Kinga anan kuwa ai ba tattali ,wata Kuma ita ba ita ke barnar ba yaranta ne masu jarabar barna Kuma zakiga Bata damu tayi musu fada ba tana kallonsu yara ne zasu wuni tsalle tsalle kan kujeranta sukoma barke kujerun wasu kiga su cika jikin bango da rubuce rubuce wasuma fa namiji be Isa yayi ajiyar takardunsa ba shida gidansa akwae wacce tabar yaran suka barka Important doc na babansu kuma Yana ban labari yazo Yana Mata magana ko ajikinta balle ma tayiwa yaran fada ,wlh akwae matan da idan sukace zasuzo gidanki sekinji kirjinki ya buga tsabar barnar yaransu don kinsan ranar de se anmiki asara ko asaka ki gyaran dasae kin gaji ,Sam wasu matan Basu kyautawa wlh wata ma zakiga barnar kayan abinci Sam hr gobe batasan ma aunin gidanta ba sede anzubar da abinci abola wata ma wae mugunta ce irin ta kishiyoyi itama Bari abarnatar da abincin 
    Abangaren rashin tattali dole kazanta tashigo don wasu matan fa rashin tattala kayannasu ne zakiga gata matar aure Amma ko kan bed dinta bazaki iya kwanciya ba common bedsheet Bata wankewa da kyau zakiga duk sun kode sun mutu ,wata Kuma arayuwarta dakinta ne kullum komi ya lalace hatta socket ita da yaranta Basu iya barinsa yazauna lafiya se sun Bata ,sun Bata tv ,DVD komi de akwae wacce nagani har labule seda yaranta suka yagashi kuma bata damuba Kuma gobe acewa namiji ya chanja idan yace bazae chanja ba shikenan ace namiji marowaci kobe kula da iyalinsa wata Kuma cikin kishiyoyi take komi aka siya muku tare naki yariga lalacewa ke ga uwar yara baki San yanda Zaki controlling dinsu ba wata ma setace Miki wae haka Allah yayi yaran masu barnar tsiya karyane Shi yaro Babu yanda za ayi kakasa juya kayanka Yana yaro hr sede idan ya girma 
     Akwae Kuma matan da arayuwarsu matsalarsu ta kudi ce kudi be isansu duk kokarin da namiji ze yi abanza zakiga namiji hr tsoron kudinsa yashiga hannunta yakeyi don yasan abanza zasu susuce wata sam Bata San me ake nufi da ajiya ba ita de inde taga kudi akashe ahaka zatayi ta tunzura mijin da shawarwari kudadensa suyi ta salwanta abanza 
    Wata Kuma karyar zamani ta dorawa kanta mijinta bekai matsayin wasu ba seta yi ta turashi tana hangen rayuwar wasu tasaka shi yaje yadinga kashe last change dinsa Yana siyo Mata Abu misali irin matan da mazajensu kebin shawararsu sekiga tasakashi yasiya Mata wani abun dazae je yatakura kansa koma yaci bashi wae don ya faranta Mata Suma fa Mata gaskiya dasauransu dole se ana gyarawa ,wannan maganar tattali kisani cewar zakiyi ne don gobenku don ki gyara muku future idan ma kina tunanin Kar kiyi gini wata tazo ta Mora kikoyi tattalawa don kanki hakanan shikansa almubazzaranci damukeyi don ganin akwae. Koma mugunta Babu kyau 
    Allah dakansa acikin Al qur ani me girma Yana cewa "innal mubazzirina kanuu min ikwaati sshayaadiinn ......zuwa karshen aya " 
     Waton lalle su masu almubazzaranci sun kasance Yan uwane na shaidaanu 
    Saboda HAKA mudinga kiyayewa kodon ma mutsira mu rabauta in ma kina tunanin shi namiji ba atausaya mishi karshe kishiya zatazo ta mora to kiyi don Allah
Post a Comment (0)