*JININ AL'ADA YA DAUKE MATA BAYAN ASUBAHI*
*Tambaya*
Assalamu Alaikum dan Allah malam inada tambaya matar datake jinin al'ada sai ya dauke mata da Asuba to wani sallah zata rama kafin asuban kokuma ya dauke karfe biyu shikuma wani sallah zata rama kafin tayi Azahar?
*Amsa*
Wa'alaykumussalam
Idan jini ya dauke kafin fitowar alfijiri toh za'a rama sallar isha'i..
Idan kuma ya dauke da karfe biyu toh zata yi sallar azahar ne kawai.
Wallahu a'alam
*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*
15/03/2019
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```