HUKUNCIN AZUMIN WATAN RAMADAN


*HUKUNCIN AZUMIN WATAN RAMADANA* 
 
Azumin Watan Ramadana rukuni ne daga cikin rukunnan Musulunci, Musulmi gaba dayan su suna matsayi daya wajen sanin hakan; domin yana daga cikin abubuwan da suke dole a san su a Addini. 
Kuma yana zama wajibi ne ga kowani Musulmi, mai hankali, wanda ya Balaga, mai lafiya, mazaunin Gida, da ne ko Bawa, Namiji ne ko Mace, amma badda wacce take fama da Jinin Haila ko kuma Jinin Haihuwa.
 
Yana daga cikin dalilan da suke bayani akan wajabcin Azumi, fadar Allah – madaukaki: 

(Ya ku waɗanda kukayi Imani, an wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta shi ga waɗanda suka gabace ku don kuji tsoron Allah)             
[Suratul Bakara: 183].
 
Kuma Allah – tsarki da daukaka sun tabbata gare shi yace:
 (Watan Ramadana wanda aka saukar da Al-Ƙur’ani a cikin sa a matsayin shiriya ga Mutane da hujjoji na shiriya da rarrabewa tsakanin Ƙarya da Gaskiya. Saboda haka, wanda ya halarci Wata daga cikin ku, to ya Azumce shi………) [Suratul Bakara: 185].
 
A cikin Sunnah kuma Manzon Allah ﷺ yace: 

“An gina Musulunci akan rukunnai guda biyar, Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya ame cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne, da tsayar da Sallah, da bayar da Zakka, da yin AZUMIN WATAN RAMADANA, da ziyartar Dakin Allah”. 
[Bukhaariy da Muslim ne suka riwaito shi daga Sahabi Abdullahi ɗan Umar]  

#Article_03
#Asha_Ruwa_Lahiyah

Domin samun jerangiyar wa'innan Articles, kasance da mu a
https://t.me/annasihatvchannel
Post a Comment (0)