JIKIN ƊAN ADAM 05

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 05🍍🍊*

*(Fitowa ta Biyar)*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

Addini dai mai sauqi ne, Allah SW ba Ya daura wa bayinsa abin da ba za su iya ba, duk wata shari'a da ka gani an dora mana ita ne gwargwadon qarfimmu, shi ya sa in Allah SW Ya saukar da shari'a ba Ya bari a yi qari don neman lada, Annabi SW ma ya ce Allah Ya yi shuru a kan wasu abubuwan don rahama ne gare mu ba don Ya manta ba, ya kuma hana a yi bincike a kai, wannan zai fassara ayar da take cewa kada ku yawaita tambaya a kan hukuncin da ba a saukar muku ba, in da za a saukar din sai ya buwaye ku.

Kenan ba gwaninta ba ce ko jarumta ka kawo abin da ba a farlanta maka ba, ko ba a ma sanya ka ka yi ba, misali:-

1) Mutum ya aza wa kansa cewa shi fa kullum azumi zai yi, don yana neman lada, sai ya kasance babu wani lokaci da ya tanadar wa kansa don cin abinci, haqiqa jikinsa ma yana da haqqi a kansa, dole ya ba shi haqqinsa na abinci da jima'i, idan jiki bai wadatu da lafiyayyen abinci ba ko yin azumin nan gaba zai iya zama masa matsala, sannan hakan zai iya fitar masa da sha'awar saduwa da mace.

Idan aka kai ga an sami wani dalilin da zai sa a kauce wa sunnar ma'aiki wajen tabbatar da Rahabaniyancin da ba shari'ar muslunci ba ne, to tabbas an saki hanya, Annabi SAW ba wanda ya kai shi tsoron Allah, amma duk da haka matansa tara ne a lokaci guda, kuma yakan zaga su gaba dayansu da wanka guda [a Bukhariy], kenan mutum ya nemi duk abin da Allah SW ya halasta masa na cin abinci da jima'i, sannan ya sami lokaci na bautar Ubangijinsa.

2) Da yawa za ka taras an dawo masallaci amma wasu ba sa cin abinci wai suna azumi, wannan kam haramun ne Allah Ya haramta, ba a yin azumi ranar sallah, koda kuwa qarama ce ko babba, in mutum ya azumci Ramadana to sallah rana ce da za a ci a sha don qarfi ya dawo wa mutum, ya sami sakewa, jikinsa ya ginu ya sami qarfi, haka bayan babbar sallah, koda mutum bai yi azumin tadawwa'i ba sai na Arfa, ko ma bai yi su duka ba, bai halasta ba ya yi azumi ranar babban sallah.

3) Hatta bayan babbar sallar, duk da cewa malaman mazahabobi sun yi musayar fahimta, amma a qarshe dai ya bayyana cewa ba a yin azumi bayan sallah na ranakun 11, 12, 13 ana kiran wadannan ranaku ne na Tashriqi, wato ranakun yin baron nama, a shanya ya bushe don kar ya rube, Annabi SAW ya ce ranaku ne na ciye-ciye da tande-tande, bai halasta mutum ya dauki azumi ba, gwara dai ya bi shari'a don neman zama lafiya.

4) Matar aure ma da take tare da maigidanta a wuri guda, bai halasta ba mace ta yi azumi sai da yardar maigidanta, don yin azumin ba tare da ya sani ba zai iya cutar da shi, ta yuwu yana da buqatarta ga shi kuma tana yin wata ibadar, haqiqa saduwar aure ma wata ibada ce wace ba ta haduwa da azumi, don haka yake wajaba mace ta nemi izinin yin azumi ga mijinta a watan da ba na Ramadana ba.

5) Macen da take jinin haila ko na haihuwa, dukansu bai yuwuwa su dauki azumi don cutar da suke fama da ita a lokacin, ko dai mai haila a sanadiyyar rubewar sinadarin da Allah SW Ya halitta a mahaifarta don zama abinci ga jariri, ko kuwa jinin da zai kwarara ga mace a sanadiyyar haihuwa, yadda aka hana maza kusantar mace mai fama da wannan jini, haka shari'a ta hana ta yin azumi.

6) Ranar da ake shakkun an ga wata ko ba a gani ba bai yuwuwa mutum ya dauki azumi, sai in yana da tabbacin cewa an ganin, ko dai shi ya gani da idonsa, ko wani ya ba shi labari, masamman yadda kafofin watsa labarai suka yawaita a 'yan tsakankaninnan, irin su Sunna tv da sauransu, in har mutum bai sami labarin ganin wata ba ba zai iya kwanciya da niyyar tashi da azumi ba, ko ya yi bai da azumin wannan ranar, in ya tashi bai ji labarin ganin wata ba to ya narki abincinsa don gina jikinsa ya fi masa.

7) Malamai da dama gwargwadon hadisai da bayanan magabata sun tabbatar da haramcin yin azumi kafin ramadana da kwana daya ko biyu, wadannan ranaku ne da mutum zai ci ya sha abin da zai gina masa jiki, ya yi tattalin kuma zuwan watan Ramadana, amma ba gwanita ba ce kamar yadda za mu yi bayani mutum ya cike watan Sha'aban sannan ya dora da Ramadana, a maimakon haka ya sami wasu 'yan kwanaki a tsakiya, haka shiryarwar Annabi SAW take.

Zamuci gaba insha Allah.

*Gabatarwa: Zauren Sunnah*

*Gamasu Sha'awar Bibiyar Karatukanmu Akan Shafukan Sada Zumunta Kamar WhatsApp da Facebook Zasu iya Bibiyarmu ta Wannan Hanyar*

*_Sai kuturo da Cikakkiyar Sallama. Da Cikakken Suna Tare da Adreshi ta Wadan nan Numbobin_*

_*WhatsApp Number*_
 +2348039103800.
 +2347065569254

_*Facebook @Zauren Sunnah*_
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/

*اللهم لا تواخذنى بما نقولوا واجعلنى خيرا مما نظنون. فقلت ما قلت. إن تك حسنة فمن الله وإن تك سيئة فمن نفسك والشيطان. وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت. وأستغفر الله 
لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرو الوبركاته

*والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته*

Post a Comment (0)