JIKIN ƊAN ADAM 09

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*🍉🍅JIKIN DAN ADAM // 09🍍🍊*

*(Fitowa ta Tara)*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

Kankana kam ba qaramin amfani take da shi ba, masamman yadda komai nata yake zama mai amfani a jiki, dubi dai bawonta da ake jefarwa, an gano cewa akwai Vitamins a ciki sosai, ga Natural salts, da Dietary fiber, ga kariya daga Oxidation, Jaridar Alhayaa ta ce bawon kankana yana da wasu abubuwan da ba ma a samunsu a cikin tuwon kankanan, a lokacin da mutum zai jefa bawon kankana cikin shara tabbas yana yin asarar wani sinadari mai suna Sitrulline.

Shi wannan sinadari shi ne yake juyawa a yayin aikinsa a jiki zuwa Arginine wanda yake taimakon jini ya sake, irin wannan aikin ne qwayoyin Viagra suke yi domin taimakon maza, a zahiri in muka ce bawon kankana ba zallar koren muke magana ba a'a farin cikinta ne da bawon koren yake manne da shi, a cikinsa ne ake samun sinadarin Sitrulline din, wani bincike da qasar China ta yi ya nuna cewa bawon na kankana yana maganin abu biyar: Hawan jini, Inflammation na qoda, gaza yin fitsari, taruwar ruwaye a jiki da yawan atuni.

Kenan akwai buqatar kankana a kowani lokaci ko don magungunan da take yi, za ka yi mamaki in aka ce maka kankana tana magance zazzabi, da zafin jiki, takan yi maganin Cholesterol da haka ka ga za ta hana ciwon zuciya kenan ko daskarewar sinadarai a hanyoyin jini, sun ce tana maganin Rheumatism sanyin jiki da cutar Ulcer da sauran matsalolin tumbi.

In dai za a riqa cin ta da kimanin minti 30 kafin abinci, za ta rage wa mutum cin abinci da yawa, ka ga an sami sauqin Fat da Sugar kenan, idan aka hada citta da zuma da kankana za su taimaka wa mai tari, to ba shi kenan ba, duk da abubuwan nan da muka ambata mutum bai san sinadarin da jikinsa yake buqata ba, in ya yawaita wani sinadarin tabbas zai cutar da shi, dole ne ma a guji cin kankanar da aka fere ta na tsawon lokaci a bude, domin Oxygen dake cikinta zai iya gamewa da na waje, in dai ba leda aka sa don ba da kariya da kuma hana sauran qwayoyin cuta ba.

Wanda yake da cutar hanta ko matsarmama shi ma ya guje ta, haka mai cutar zawo ko radadin hanji, shi ya sa ma malamai ba sa ba mutane shawarar cin kakkana bayan abincin dare, don kauce wa tururin Gas wanda zai iya taruwa a tumbi ya takura mutum a wajen barci, a duk lokacin da mutum yake qyanqenin abubuwa to ya guji kankana don tana iya qarawa, likitoci sukan ba wa mazan da suke fama da gwaiwa shawarar kar su riqa cin kankanar don tana da sinadarin Lycopene.

Wuce gona da iri ma a wajen cin kankana zai iya haifar da matsaloli ga qwayoyin garkuwar jiki, matsalolin ciki, da canjin launin fata, ko ma ka ga kalar ta canza sabo da samun sinadarin Lycopene din a ciki, kenan akan so mutum ya ci kankana amma daidai gwargwado, yawaita cinta din har ya wuce misali zai iya haifar da matsala ba ko tantama, babu laifi kullum mutum ya ci, amma ya san cewa tana qunshe da wadannan nau'o'in sinadarai da muka riga muka ambata sai ya taqaita.

To yanzu dai abin da za mu iya dauka a nan shi ne wanda ya sayi kankana ya yi qoqari ya cire koren bayan kawai amma farinnan da muke kiransa bawon kankana wanda har muke ba wa tumaki su ci gaskiya ba qaramar asara muke tabkawa ba, duk wani namiji mai iyali yana da buqatarsa, ko ba don zaqi da sha'awa ba ko don gyaran gida, wannan shi ne mafi alkhairi sama da magungunan da magidanta suke sha, irin wadannan magungunan suna rage wa mutum qarfin gani, bawon kankana gami da kankanar qarawa suke yi, magungunan suna rage mazantakar namiji a hankali a hankali, kai kuwa ko yau ka sha kankana ka hada da qwallonta da bawonta gaba daya, ina da tabbacin za ka ba wasu labari, masamman bawon kankanan.

Sannan kuma don an ce kankana tana da mahimmanci kamar kaza da kaza ba shi ne yake nufin kullum mutum ya yi mata cin qoshi ba, i ba shakka akwai wanda yake buqatarta, akwai kuma wanda in har zai yi amfani da ita alhali yana tare da wasu qwayoyin a jikinsa wadan da ba za su karbe ta ba, ba shakka zai sami matsala ba 'yar qarama ba, babban abin da ya fi dacewa da mutum shi ne ya taqaita shanta a rana koda kuwa zai riqa sha ne kullum, don dai lafiyar jikinsa, Bahaushe ya yi gaskiya ABINCINKA MAGANINKA.

*Gabatarwa: Zauren Sunnah*

*Gamasu Sha'awar Bibiyar Karatukanmu Akan Shafukan Sada Zumunta Kamar WhatsApp da Facebook Zasu iya Bibiyarmu ta Wannan Hanyar*

*_Sai kuturo da Cikakkiyar Sallama. Da Cikakken Suna Tare da Adreshi ta Wadan nan Numbobin_*

_*WhatsApp Number*_
 +2348039103800.
 +2347065569254

_*Facebook @Zauren Sunnah*_
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/

*اللهم لا تواخذنى بما نقولوا واجعلنى خيرا مما نظنون. فقلت ما قلت. إن تك حسنة فمن الله وإن تك سيئة فمن نفسك والشيطان. وسبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا اله إلا أنت. وأستغفر الله 
لى ولكم ولسائر جميع المسلمين من كل ذنب و استغفر وه إنه هو البرو الوبركاته

*والسلام عليكم ورحمة الله وبركاته*

Post a Comment (0)