BUƊAƊƊIYAR WASIƘA ZUWA GA 'YAN UWA MATA


BUDADDIYAR WASIKA GA YAN'UWA MATA




Shawara ta garemu matan Auren da yammata da zawarawan.

Duk wadda ta tsunci kanta a dakin mijinta , to ta fuskanci cewa wannan rayuwa ce ta Reality(gaskiya)
Musamman ga masu karatun novel(littafin labaru)

Wlh karya ce tsagwaronta, 

1-mijin novel ne yake raya dare guda yana love making da matarsa🤣
Mu Kuma mazajenmu na rayuwar gsky, 30 mnts ya gama👌

2-mijin novel me kudi ne, kyakkawa, kamar shi yayi kansa, mazajenmu kuwa se dai hakuri, Dan wani ko biyar ba'a sayanshi😜

3- mijin novel ne yake gina hadaddan gida , motocin alfarma, madafan gida Ac, furniture Yan waje, firji cike da duk abun bukata, store a shaqe da komai, Amma idan ze fita ze bawa mata 5k kullum🤔

4-mijin novel shi ne mace zatawa iskanci, Amma yazo lallashi harda kukansa, saboda kullum se ya kusanci matarsa sau bakwai ko fi🤦‍♀️
Yayinda namu mazan se wani yayi fin sati👍

5- mijn novel ne me Kai mace Dubai da indiya honey moon, kyautar gwal, motar alfarma,gida, company, ds.

🙏 Ina rokonku yan'uwana mata, mu dawo hankalinmu, mu rungumi samu da Rashin miji, mu daina hararo wa ranku shirmen kagaggun labaru
(An San kowa nason jin dadi, se Wanda be samu ba)
 Mu tarbiyanci yayenmu, se su zamar mna sanyin idaniya, mu nemi lahirar mu ko ma dace acan, mu kyautatawa mazajenmu da duk Wanda ya rabemu(kamar dangin mu ko dangin miji, makota ds) shine sadidan maganin mallaka.

Yanmata ku hankalta, if baki da gashin wance, ku tsaya matsayinku, miji na gari yafi komai dadi a abokin rayuwa.

Kuna karantawa a novel saurayi ya dinga ma budurwa manyan kyaututtuka ko?
To a zahiri me sakin hannu da kyautatawa ne ze yi miki xuwa zance uku, a na hudun ya baki 2k, sabida iyakar karfinsa kenan, wani kam se yai goma be bki ko sisin sa ba, balle mota ko diamond Ring.

Kun karanta ran first night suna kyauta ko, a zahiri me sanin ya kamata ne ze sa miki albarka, 
Kun ji ance har wanka su ke yiwa matan ko? To in kin sami Dan Albarka shine ze dafa ruwa ya kaimu Miki toilet.
Kudin cefanen mijin zahiri wlh idan yana da awonsa da komai da komai, Dan dai Dan kayan miya da nama ko kifi zuwa salak, bakin mutum biyu 500 ce, wataran ma bata samuwa, se dai ya bki hakuri.

Ku aje shirme da wasiqar jaki, da kin samu Wanda ze rufa Miki asiri ya killaceki s gidansa, matukar yana da addini, sana'a👍 , to ki manta duk wani buri kiyi aurenki da niyya me kyau, se Allah ya dubeki.

Mu Kuma matan aure, duk wadda ta raina sbun da tke dashi, Allah ma cewa yyi Wanda ya gode qara masa zey,
Ku tambayi zawarawa yanda suke jin gashi, Koda kuwa a dakin uwarta tke, 

Addu'ar mace ga miji kamar yankan wuqa tke.
Mu dage da musu addu'a, duk mugun halin mijinki befi qarfin Allah b, Dan hka hadashi da shi.

Allah yasa mu dace
Idan mun dace mu dafe💸💵💴

GYARAN MATA DOMIN MAZA WhatsApp group

Maman khaleed
Post a Comment (0)