KO KASAN WANDA YAFI KOWA KUSANCI DA MANZO RANAR ALQIYAMA??)
Sahabi Abdullah bin Mas'ud Allah ya kara yarda dashi yana cewa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yana cewa "Wanda yafi kusanci dani ranan tashin qiyama shine wanda yafi yawaita mun salati".
صحيح ابن حبان ٩١١
Shaikh Ibnu Baaz Allah ya masa rahama yake cewa "Ai Wanda yafi kowa kusanci da manzon Allah shine Wanda yake yawaita yimasa salati saboda imani dashi da kuma soyayyarsa gareshi da kuma koyi da shari'arsa".
مجموع الفتاوى
# zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah