KOWA SAI YA YI NADAMA, KOWA SAI YA YI KUKA


*KOWA SAI YAYI NADAMA KOWA SAI YAYI KUKA*

24/02/2020

Daga Dakta Ahmad Ibrahim BUK

A duk lokacin da aka rufe kowacce kofa tsanani yayi yawa, dole kowa ya nema kansa mafita. Idan aka ce aiki sai dangata shi kuma mara gata zai nemawa kansa mafita mai kyau ko mara kyau. Ka yi duk yadda zaka yi ka ci zabe amma yawo ya gagare ka. 

Bafulatani da bai damu da waye Shugaban kasa ko Gwamna ko Sanata ba yana rayuwa a daji daga shi sai shanunsa, bai damu da kwalta ko lantarki ba, ya samar da nama da madara da man shanu, an tabo shi ya nemi mafita ta hanyar kama mutane a ba shi kudi.

Mutum har cikin gidansa za a je a sace shi a sace iyalansa, yawo a manyan motoci ya gagari Shugabanni. Aiki ya zama daga 'ya'yan masu mulki sai 'ya'yan masu Naira. Kowa yana ji yana gani an rasa zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Zalinci da rashin manufa ya sa wadanda ya kamata su samar da aminci suna neman koyawa mara gata ya nemi gata ta hanyar tayar da hankali da barazana ga rayukan mutane. Yau AK47 na neman zama abinda mara gata zai nema don nemawa kansa gata a wajen masu gata. Yara kanana sun iya sarrafa AK47 sun kuma san inda zasu nema su samu.

Duk dabara da azancin mutum bai isa ya gyara wannan matsala ba har sai an gyara hanyoyin da suka haifar da matsalolin. Allah ba ya jefa mutane a bala'i haka kawai har sai sun aikata abinda zai janyo bala'in. Allah baya shafe alheri da jin dadin mutane har sai idan su suka aikata abinda zai shafe alherin.

Kowa sai yayi nadama kowa sai yayi kuka matukar ba a yarda akwai matsala an kuma yarda a gyara ba.

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*
WhatsApp 07036073248
Post a Comment (0)