MUYU ƘOƘARIN RAYA WANNAN SUNNAH MAI GIRMA
YIN ALWALA LOKACIN KWANCIYA BARCI
Yana cikin Sunnar Annabi ï·º tabbatacciya yin alwala lokacin kwanciya barci,ko kwanciya barci da
Alwala,lokacin Barci, Annabi ï·º yayi a aikace.
Manzon Allah ï·º yana cewa:
*(Ku tsarkake wannan jiki,sai Allah ya tsarkakeku, domin babu wani bawa da zai kwana cikin tsarki (alwala) face ya kwana tare da Mala'ika a kusa da shimfidarsa,babu wani motsi da bawan zaiyi acikin wani lokaci na dare face yace:"Allah ka gafartawa wannan bawan naka,domin ya
kwana cikin tsarki")*.
@Alban yace Hadisine mai kyau:Saheehut Targheeb
●Annabi ï·º ya fada ga Barra'h BN Azem R.A:
*(Idan kazo wajan kwanciyarka,sai kayi alwala,alwala irinta Sallah,Sannan ka kwanta a bangaran jikinka na dama....)*
@Bukhari da Muslim.
¤Ibn Hajar al'asqalany yana cewa:Mustahabbine
jaddada alwala lokacin kwanciya barci,koda kuwa alwalar mutum bata karyeba,Musammama idan mutum yana da Hadasi.
@Fathul Bary.
Allah ne mafi sani.