WALLAHI SAI MUN NEMI SULHU DA ALLAH!

WALLAHI SAI MUN NEMI SULHU DA ALLAH!!

MANYAN HANYOYIN DAKE TAIMAKAWA WURIN YAYE BALA'I:

1- TSORON ALLAH (Taqawa)! Tsoron Allah sababi ne mai karfi da ke yaye bala'i da kuma kawar da masifa bayan sun sauka ga bawa/bayi.

Allah Na cewa: Kuma duk wanda ya ji tsoron Allah to tabbas Allah Zai kawo masa mafita.
DON HAKA MU KARA KOKARI WURIN NESANTAR AIKATA ABIN DA ALLAH BAYA SO
DA AIKATA ABUNDA YAKE SO.

2- ADDU'A: Ibnul Qayyim ya fadi irin albarkar da addu'a ke da shi inda ya ce:" Addu'a na cikin magunguna mafiya anfani, saboda ita addu'a bata jituwa da bala'i, ita ce take tunkuÉ—e shi kuma take magance shi, haka nan ita ce take hana bala'i sauka, kuma ita ce take zama sanadin yayewa ko samun rangwamensa idan ya sauko(kamar yadda ya tabbata a nassoshi dadama).

3- YAWAN ISTIGFARI (NEMAN GAFARAR ALLAH): Allah da kansa yana cewa: Ubangijinka bai zanto mai yi musu azaba ba alhali kana cikinsu -Ya kai Manzon Allah- haka nan ubangijinka ba mai azabtar da su ba ne, ALHALI SUNA ISTIGFARI. 

DON HAKA SHI ISTIGFARI GARKUWA NE DAGA AZABA DA BALA'I KODA KUWA SUN SAUKO.

4- YAWAITA YIN SALLAR NAFILA: Allah Yana cewa: Ku nemi taimako ta hanyar yin hakuri da kuma yin sallah....
Kamar yadda Manzon Allah ya nusar da yin haka a cikin hadisan kisfewar rana ko na wata inda ya ce in haka ta faru to KU ZABURA KU YI SALLA HAR ALLAH YA YAYE MUKU ABIN DA YA SAME KU...

5- YAWAITA YIN SADAKA: ko shakka babu sadaka na daga cikin mafiya muhimmancin sabuban yayewar bala'i, Ibnul Qayyim na cewa: Hakika sadaka na yeye bala'i ga mutum koda kuwa kafiri ne ko fajiri(kamar yadda nassoshin Qur'ani suka bayyana), ku dubi yadda Manzon Allah ya yiwa mata wasiyya cewa su ringa sadaka saboda su tseratar da kansu daga bala'i mafi girma na azabar wutar jahannama.

DON HAKA MU YI KOKARIN MAYAR DA HANKALI KAN SABUBA NA SHARI'A SU NE MAFITA TA FARKO.

ALLAH KA YAFE MANA GANGANCIN MU DA KUSAKURAN MU DA LAIFUKAN BOYE DA NA SARARI, DA WANDA MUKA YI MUNA SANE DA WANDA BA MU SANI BA.

YA ALLAH KADA KA KAMA MU DA MIYAGUN AYYUKAN MU DA KUMA LAIFUKAN DA WAWAYEN CIKIN MU KE AIKATAWA.

Copied

Post a Comment (0)