LADUBBAN DA MAI AZUMI YA KAMATA YA KULA DA SU

Article 005//

LADUBBAN DA MAI AZUMI YA KAMATA YA KULA DASU

Wadannan sune dunkulallun ladubban da nassoshi na Shari’a suka zo dasu kuma suka kwadaitar wa akan su, sai dai a Yau zamu dauke wasu ne daga cikin muyi bayanan su, kuma ya kamata ga kowani mai Azumi ya kula dasu kulawa ta musamman, lokacin da yake dauke da Azumi a bakin shi.

LADABI NA FARKO: KIYAYEWA AKAN SAHUR, TARE DA JINKIRTA SHI

Saboda fadar Annabi ï·º: “Kuyi Sahur domin shi Sahur acikin sa akwai albarka”.
[Bukhaariy da Muslim ne suka riwaito shi daga Sahabi Anas É—an Malik]

Ba hakanan ba kadai, Annabi ï·º ya sanya cin Sahur yana daga abunda yake bambanta ma’abota Musulunci daga Yahudu da Nasara, sai Annabi ï·º yace: “Bambancin da yake a tsakanin Azumin mu da Azumin Yahudawa da Nasara, shine cin Sahur”.
[Muslim ne ya riwaito shi daga Sahabi Amru É—an Ass]

Bayan haka kuma, Sahur yana sanya nishaÉ—i da walwala ga mai Azumi, sannan yana kara Lada da albarkar Azumi, kuma dukkan Annabawan Allah suna yin Sahur, kuma Allah da Mala'ikun Sa suna yin Addu'a ta musamman ga masu yin Sahur kamar yadda Imamu Ahmad ya riwaito daga Sahabi Abu Sa’eed.

Ina ma da ace Musulmi ya sanya Busasshen Dabino a matsyain abun Sahur dinshi, saboda koyi da maganar Annabi ï·º: “Madallah!! da Sahur din Mumini da yayi shi da Dabino”. [Abu Dawuda ne ya riwaito shi daga Sahabi Abu Hurairah]
Idan ma bai samu Dabinon ba, to yana iya yin Sahur dinshi da duk abunda ya samu, abunda dai ake umurtar shi kada yabar yin Sahur din, domin albarka mai yawa da yake dashi kamar yadda muka fada.

LADABI NA BIYU: YIN ASUWAKI

Yin asuwaki yana daga cikin Sunnoninn Annabi wadanda yake kula dasu, bayan nan kuma yake kwadaitar da Al’ummar Shi akan yin ta, ba haka ma kadai ba, ya kasance yana umarni ne da a kula dasu yadda ya dace, Manzon Allah ï·º ya kasance idan ya tashi daga Bacci yana goge Bakin Shi mai albarka da Asuwaki, kuma yana farawa dashi da zaran ya shiga Gida, haka ma a gurin Alwala, da sanda zaiyi Sallah.

Shi ne ma yake cewa Annabi ï·º: “saboda gudun kada na tsananta ma Al’umma ta, da na umarce su dasu dinga yin Asuwaki a sanda zasuyi kowace Sallah” [Bukhaariy da Muslim ne suka riwaito shi daga Sahabi Abu Hurairah]

Kuma ya sake cewa Annabi ï·º: “Asuwaki yana tsarkake Baki, haka kuma yana samar da yardar Ubangiji” [Imamun-Nasa’i ne ya riwaito shi daga Uwa Muminai Aishah]
Don haka ya halasta ga Musulmi ya kiyaye yin Asuwaki a kowani hali ya kasance, yana Azumi ne koma baya yi, babu bambancin wajen yin Asuwakin ga mai Azumi yayi shi da danyen icce ko busasshe, a farkon yini ne ko a karshen yini, duka ya halasta zai iya yi.

Post a Comment (0)