LADUBBAN MAI AZUMI
A yau zamu cigaba da bayani ne a inda muka tsaya bayan mun tattauna akan cewa wanda yake Azumi ya bayar da muhimmancin yin Sahur a koda yaushe, kuma mukaji cewa Sahur yana da albarka matuka kwarai da gaske, abunda ake cewa albarka shine: Alkhairi mai tarin yawa kuma mai faɗi wanda baya gushewa, don haka Sahur yana da albarka, lokacin mai albarka ne abincin mai albarka ne, bayan nan sai kuma mukaji bayanai akan Asuwaki yana daga cikin Sunnonin Annabi bayan haka ma yana da fa’idoji masu yawa, to yau zamu cigaba Insha Allahu.
LADABI NA UKU: NESANTAR DUK ABUBUWAN DA SUKE KORE DALILIN DA YASA AKE YIN AZUMI
Allah madaukaki yace: (Ya ku waɗanda kukayi Imani, an wajabta muku Azumi kamar yadda aka wajabta shi ga waɗanda suka gabace ku don kuji tsoron Allah) Suratul Bakara: 183.
Babban Malamin Tafseerin nan Al-Imamu Ibn Katheer yace: “Allah yana mai Magana da Muminai na wannan Al’umma, kuma yana umurtar su da yin Azumi, shine: kamewa daga barin cin abinci, da abun sha, da kuma yinsa ta hanyar tsantsan ta niyya ga Allah mabuwayi da daukaka saboda abunda yake cikin sa na tsaftace zuciya da tsarkake ta, da kuma tace ta daga cakuduwa da munanan abubuwa, da halaye marasa kyau”.
Shi dai Musulmi a koda yaushe ana umurtar shi da ya samu tsari daga aikata abubuwan da aka hana, tun daga munanan maganganu da munanan ayyuka, to yaya kenan idan ya kasance yana Azumi a Watan Ramadana?
Hadisai masu yawa sun zo game da wannan ma’anar daga Annabi ﷺ, daga cikin su shine fadar Sa cewa: “Azumi ba ya takaita bane kadai da barin cin abinci ko shan abun sha, lallai abunda yake Azumi shine barin mummunan wasa da yin kwarkwasa, idan ya kasance a yinin da ɗayanku yake Azumi, wani ya zagesa, to kada ya rama, yace masa ni mai Azumi ne, ni mai Azumi ne”. [Ibn Khuzaimah ne ya riwaito shi daga Abu Hurairah]
A wani Hadisin kuma cewa Annabi ﷺ yayi: “idan ɗayanku ya wayi gari yana Azumi, kada yayi kwarkwasa kuma ya yi wauta, idan wani ya zagesa, ko wani ya dokesa, to kada ya rama, yace masa ni mai Azumi ne, ni mai Azumi ne”. [Muslim ne ya riwaito shi daga Abu Hurairah]
Hakika tsoratarwa mai tsanani yazo ga wanda bai bar abubuwan da suke kore asalin dalilin yin Azumi ba, har Annabi ﷺ yace: “duk wanda bai bar zance na karya ba, da aiki da ita ba, to bashi da bukata a wajen Allah ya bar cin abincin shi ko shan abun shan shi ba”. [Bukhaariy ne ya riwaito shi daga Abu Hurairah]
Babu makawa lallai nesantar abubuwan da aka hana yana lizimta akan kowani Musulmi mai Azumi ya kawar da kai idan dan uwansa yayi masa ba daidai ba ko kuma kuskure, ya kawar dakai daga munantawar masu munanawa.
✍🏽@AnnasihaTv