LADUBBAN MAI AZUMI: GAGGAUTA BUƊA BAƘI


*DAY 07* 
 ```RAMADAN ARTICLES``` 

 *LADABI NA HUDU: GAGGAUTA BUƊA BAKI* 
Ya kai dan uwana Musulmi ka gagaguta buda-baki da zaran Rana ta fadi, domin yin haka tsantsanta biyayya ce ga Sunnar Manzon ka (SAW) wanda Allah yace maka shine kyakkyawan abun koyin ka, kuma gaggauta buda bakin sabawa ne ga Yahudu da Nasara, domin su suna jinkirtawa ne jinkintawar su kuma tana da lokaci, wato bayyanar taurari, kuma a cikin bin hanyar Manzon Allah (SAW) akwai bayyana alamomin Addini, dad a tinkaho da abunda muke kai na shiriya wanda muke kaunar mutane da Aljanu su hadu a kansa, daga cikin fadar Annabi (SAW): 
“An Karbo Hadisin Ingantacce daga Sahal ɗan Sa'ad (Allah ya kara masa yarda) Lallai Manzon Allah ﷺ yana cewa:

 ```“Mutane basu gushewa suna cikin alkhairi, matukar suna gaggauta buɗa baki”``` 
[Bukhaariy da Muslim]
Idan rana ta faɗi mai Azumi ya yi buɗa baki, jinkirta buda baki har duhu yayi yin haka bidi'a ce, kamar yadda muka ji Manzon Allah ﷺ ya fadakar damu gaggauta buda bakin yana daga cikin abubuwan da suke kawo mana alkhairai.
To anan, ya dace agare mu musan wasu ladubba da suke da alaka dashi buda baki musamman; domin shi mai Azumin ya lizimce su, saboda sun tabbata daga Annabi (SAW).
 *BUDA BAKI KAFIN SALLAR MAGRIBA:* 

Manzon Allah (SAW) ya kasance yana yin buda baki kafin yayi Sallar Magriba ne saboda gaggauta buda baki yana daga halayyar Annabawa, saboda fadar Anas Dan Malik: ban taba ganin Manzon Allah ba: ban taba ganin Manzon Allah ko sau daya ba yayi Sallar Magriba ba , face sai da yayi Buda Baki, ko da shan ruwa ne.
 *ABUNDA YA KAMATA MAI AZUMI YA FARA BUDA BAKI DASHI:* 

 Manzon Allah (SAW) ya kasance yana kwadaitarwa game da yin Buda Baki da Dabino, saboda fadar Sahabi Anas ɗan Malik (Allah Ya ƙara masa yarda) yace: Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya tashi yin buɗa baki yana samun ɗanyu daga ‘ya’yan itatuwa sai yasha Ruwa dasu tun kafin yayi Sallar Magriba idan bai samu irin wadannan ɗanyu ba to sa’annan sai ya nemi Dabinai idan ya zama bai samu Dabinai ba sai ya samu Ruwa yasha.

  [Abu Dawuda ne ya riwaito shi kuma Nasiruddeenil Albaniy ya inganta shi]
 *ABUNDA MAI AZUMI ZAI FADA LOKACIN BUDA BAKI:* 

Ka sani ya ɗan’uwa mai Azumi, Allah yayi mana gamo-da-katar tare da kai, saboda bin Sunnar Annabin mu (SAW) cewa kana da wata Addu’a karbabbiya, saboda haka kayi amfani da wannan dama, kayi kana mai amincewa za’a amsa maka ka sani cewa Allah bay a karbar Addu’a daga zuciyar da take gafalalliya mara natsuwa, ka roki Allah abunda kake bukata na alheri don ka sami alherin duniya da na Lahira.
Sannan mai Azumi bayan ya kammala buda bakin sa zai fadi wannan Addu’ar kamar yadda Sahabi Abdullahi ɗan Umar (Allah Ya ƙara masa yarda) yace: Manzon Allah ﷺ ya kasance idan ya sha Ruwa ga irin Addu’a da Zikirin da yake yi: “Zhahabaz Zama’u, Wabtallatil Uruƙu, Wathabatal Ajru In sha Allah”. 

[Ma’ana: Ƙishin Ruwa ya tafi, Jijiyoyi sun Miƙe, Lada kuma in Allah yaso ya tabbata].
@AnnasihaTv
Post a Comment (0)