MARABA DA WATAN RAMADAN 6


*MARABA DA WATAN RAMADAN*

             [ 6 ]

FA'IDODIN AZUMI TARE DA FALALARSA


Da yawa daga cikin ayoyin Alqur'ani da Hadithan Manzon ALLAH (SAW) sun bayyana Fa'idar Azumi da kuma Falalarsa, kamar haka:

• SAMUN GAFARA DA LADA MAI GIRMA GA MASU AZUMI MAZA DA MATA:

ALLAH mai Girma da daukaka Yace:" lallai musulmai maza da musulmai mata, da muminai maza da muminai mata, da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu haquri maza da masu haquri mata, da masu tsoron ALLAH maza da masu tsoron ALLAH mata, da masu sadaqa maza da masu sadaqa mata, da masu azumi maza da masu azumi mata da masu tsare farji su maza da masu tsare farjinsu mata da masu ambaton ALLAH maza da masu ambaton ALLAH mata,ALLAH yayi musu tattalin gafara da sakamako mai girma" .

(surah ta 33 aya ta 35)

Kunga a wannan ayar azumi tazo acikinta.

• AZUMI GARKUWA NE DAGA WUTA KUMA KARIYA CE DAGA SHA'AWA:

Kamar yadda fiyayyen halitta Annabi (SAW)

Yace: " ya ku taron samari wanda duk ya samu hali daga cikinku to yayi aure, domin shine mafi runtsewa ga ido kuma mafi kiyayewa ga farji, wanda kuma bai zamu iko ba to sai yayi Azumi domin shi Azumi kariya ne agareshi" .

(Bukhary 4/109, Muslim 1400 daga Ibn Mas'ud R.A)

Kuma Manzon ALLAH (SAW) Yace: " Babu wani Bawa da zai azumci wani yini saboda ALLAH, face sai ALLAH ya juyar da fuskarsa daga barin wuta da Nisan shekara saba'in" .

(Bukhary 6/35, Muslim Hadith mai lamba 1153)

A wani fadin nasa kuma: "Azumi garkuwa ne wanda Bawa ke kariya da ita daga wuta" .

(Ahmad 3/241)

• HAKA KUMA AZUMI NA ZAMA DALILIN SHIGA ALJANNAH GA MAI YINSA:

Tunda mun San cewa azumi yana nisantar da mai yinsa daga wuta to lallai kuma yana kusantar da mai yinsa zuwa ga aljannah.

Hadithin Abu Umamah Al-bahiliy ya tabbatar da haka yayin da Yace" sai nace Ya Manzon ALLAH (SAW) ka shiryar dani ga wani aiki wanda zai shigar dani aljannah, sai Manzon ALLAH (SAW) Yace na umurceka da Azumi babu tamka agare sa" .

( Bukhary 4/95, Muslim 1156)

• ALLAH (SWT) YANA CIKAWA MASU AZUMI LADAR SU BA TARE DA IYAKANCEWA BA:

Wannan wata falala ce da fa'ida mai girma wadda ta cancanci masu azumi. Duba ga wannan hadith din:

Abu-hurayrah (RA)

Yace: Manzon ALLAH (SAW) Yace: "dukkan kyakykyawan aiki da dan Adam yayi ana ninja masa ladar aikin har zuwa ninki goma ko zuwa ninki 700, amma sai ALLAH (SWT) Yace:

shi Azumi nawa ne kuma Ni me sakawa a kansa" Wannan Hadith yana tabbatar mana da cewar ALLAH ne kadai yasan yawan ladar da mai yin azumi yake samu.

• AZUMI YANA CETON MAI YINSA A RANAR ALQIYAMA:

"Azumi da Alqur'ani suna ceton Bawa a ranar alqiyama, Azumi zai ce: Ya Ubangijina na hana bawanka cin abinci da kuna sha'awarsa domin haka ka bani cetonsa, Alqur'ani shima zai ce: nima na hana masa barci da dare yana karanta ni, domin haka ka bani cetonsa, sai ALLAH ya basu ceto sai su ceci wannan Bawa.

(Ahmad 6626, Hakim 1/554)

• ALLAH (SWT) YA KE6ANCE WATA QOFA DAGA QOFOFIN ALJANNAH:

Haqiqa ALLAH (SWT) ya ke6ance wata qofa daga cikin qofofin aljannah ga masu azumi kuma ya ambace ta da suna "RAYYAN" .

Manzon ALLAH (SAW)

Yace:"lallai acikin Aljannah akwai wata qofa ana ambatonta da Suna Rayyan, a ranar qiyama masu azumi suna Shiga ta cikinta babu mai Shiga ta cikinta sai su, idan suka qare Shiga sai a rufe qofar, kuma duk wanda ya Shiga ta wannan qofar za'a shayar dashi abin sha wanda bazai sake qishin ruwa ba har'abada" .

(Bukhary 4/95)

• AZUMI YANA ZAMA KAFFARA:

daga cikin falalar da Azumi ya ke6antu dashi ALLAH (SWT) ya Sanya shi a matsayin kaffara ne ga wasu laifuffuka.

ALLAH YA DATAR DAMU DA ALKHAYRAN DAKE CIKIN WANNAN WATA (Ameen)

Zamu chigaba da yardar Allah...

Faridah Bintu Salis
(Bintus-Sunnah)

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

Don kasancewa damu a shafin telegram sai a danna koren rubutu👇 (link) 

https://t.me/miftahul_ilmi

 →Ga masu sha'awar Shiga Zauren *MIFTAHUL ILMI* WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248
Post a Comment (0)