AL-AQEEDA AL-ISLAMIYYA
_________________
Rubutu (02)
•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
✿ Masu siffantawa basa iya siffanta haÆ™iÆ™anin siffarsa (Allah Ta'ala), masu tinani kuma basa iya gano komai da yake kewaye dashi, suna i'itibarine da ayoyinsa amma basa iya yin tinani akan hakikanin zatinsa, basa riskar komai acikin ilminsa sai abunda yaga dama, kujerarsa ta yalwaci sammai da kasai, kula dasu (sammai da kassai) din ba abun wahala Bane agareshi, lalle shi madaukakine kuma Mai girma, masani ne kuma Mai bada labari, Mai jujjuya al'amurane kuma Mai iko akan komai, Mai jine kuma Mai gani, madaukaki Mai girma. Kuma lalle shi yana kan al'arshinsa Mai daraja da zatinsa, amma ilminsa ya isa ko ina, shi ya halicci mutum kuma yasan abunda yake kullawa acikin zuciyarsa, kuma hakika shi yafi kusanci izuwa gareshi sama da jijiyar wuyansa".
مقدمة ابن زيد القيرواني لكتابه الرسالة...
# ZaurenFisabilillah
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah
14/3/2020
___________________