MU SAN AZUMI A SHARI'ANCE 1

_*🌙MUSAN AZUMI A' SHARI'ANCE🌙*_(1)

MENENE AZUMI
Azumi na nufin; kamewa ga barin wani abu
Amma a shari'a (الصَّوْمُ) assaumu shi ne kamewa ga barin ci da sha da barin yin jima’i tun daga bullowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada ga Allah. 
Ubangiji madaukakin Sarki yana cewa:
قَالَ تَعَالَى: "يَأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ." (سورة البقرة: 183)
Ma'ana: “Ya ku wadanda kuka yi imani, hakika, an wajabta muku yin Azumi kamar yadda aka wajabta (shi) ga wadanda suka gabace ku domin ku ji tsoron Allah.” (Al- Bakara: 183).
 Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce: 
"بني الإسلام على خمس شهادة أن لا إلـه إلا الله وأن محمدا رسول الله وإقام الصلوة وإيتاء الزكاة وحج البيت وصوم رمضان" رواه البخاري ومسلم.
“An gina Musulunci a bisa abubuwa guda biyar; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah ne, da tsai da Salla da ba da Zakka da ziyartar Dakin Allah (Aikin Hajji) da azumtar watan Ramadan” (Bukhari da Muslim).
Azumin watan Ramadan rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar. Kuma Ubangiji Madaukakin Sarki ya wajabta wa wannan al’umma azumtar watan Ramadan.
Hakika, an wajabta azumtar watan Ramadan a cikin shekara ta biyu daga hijirar Manzon Allah (S.A.W) daga Makkah zuwa Madina.

Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*USAINI AMFANIMA BABAN AMEENA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Post a Comment (0)