MU SAN AZUMI A SHARI'ANCE 11

_*🌙MUSAN AZUMI A' SHARI'ANCE🌙*_(11)

I'ITIKAFI
Ma’anar li’itikafi shi ne lazimtar Masallaci da zama a cikinsa da niyyar neman kusanci da Allah Tabaraka wa Ta’ala.
Hukuncinsa: 

Shi li’itikafi sunna ce mai karfi, kuma a goman karshe na watan Ramadan ake yin sa. Amma yin sa a wani watan mustahabbi ne.
"فَقَدْ كَانَ النَّبِي صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَعْتَكِفُ فِي كُلِّ رَمَضَانَ عَشَرَةَ أَيَّامٍ، فَلَمَّا كَانَ الْعَامَ الَّذِى قُبِضَ فِيهِ اعْتِكَفَ عِشْرُونَ يَوْمًا. (رواه البخارى)
Ma'ana:
Hakika, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana yin li’itikafi a kowane watan Ramadan kwana goma, amma da shekarar da zai yi wafati ta zo, sai ya yi kwana ashirin. (Bukhari ne ya rawaito).

Falalarsa: 
Shi li’itikafi ibada ne mai girma wanda yake tsarkake zuciya ga barin shagala da duniya kuma yana sa mutum ya dukufa wajen neman lada da kyakkyawar makoma.

Shigarsa: Ana son shiga li’itikafi kafin faduwar ranar da za a fara.

Ayyukansa: Ana son mai li’itikafi ya shagala da yin ibada kamar nafilfili, karatun Alkur’ani, tasbihi da hailala, zikiri, istigfari, salatin Annabi da sauran ayyukan bin Allah.

_*Zamuci gaba insha Allah!!*_
Rubutawa>>✍🏼
*Abubakar Salihu Kabara*

Gabatarwa_
_*USAINI AMFANIMA BABAN AMEENA*_

*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi

Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248

Post a Comment (0)