🔹 *ISTIHARA DA HUKUNCE~HUKUNCEN TA*
*05*
→Akan me Ake Istihara?
To, ana yin Istihara ce a abin da ya shafi halal, wato kamar al’amuran da suka shafi rayuwar duniya da tafiye-tafiye da sauran al’amuran da ba a san natijarsu ba, da sauran hanyoyin cimma wasu bukatu da wuraren zama da lokuta da ake da zabi a kansu da hada hannu (yin kamfani) da sauran harkokin kasuwanci da makamantansu.
Kuma ana yin Istihara a cikin abin da yake wajibi ko mustahabbi don neman zabar wanda za a yi. Misali neman ilimi mustahabbi ne, wani kuma wajibi ne, to mutum yana iya yin Istihara don zaben nau’in da zai karanta ko lokacin da zai karanta shi ko a wurin da zai je karanta shi kamar gari ko kasa ko malamin da zai yi karantun a wurinsa. Domin bawa yana da ikon zabar wurin da zai yi karatu sai ya yi Istihara a cikin hakan, yana da dama ya zabi jiha sai ya yi Istihara a kai, yana da ikon zabar makaranta, sai ya yi Istihara a kai ko makarantar da zai yi karatun.
Amma ba a yin Istihara kan neman ilimin shari’a ko in ce ilimin da ya shafi ibadar da mutum zai aikata a kashin kansa. Misali mutum ba zai yi Istihara kan neman ilimin tsarki da alwala da Sallah da aure da kasuwanci ga dan kasuwa ba da duk wani aiki na ibada da mutum zai aikata.
Neman ilimin duniya (boko) ko sana’a mustahabbi ne, don haka mutum yana da zabi kan wanda zai nema, sai ya yi Istihara kan nau’in ilimin da yake so. Haka aikin Hajji wajibi ne, duk da haka mutum yana iya yin Istihara kan yaushe zai tashi, ta ina zai tashi, ta jirgi zai tafi ko ta mota. Haka jihadi wajibi ne, amma duk da haka ana iya Istihara kan lokacin yinsa da hanyar da za a bi a yi shi da jihar da za a fuskanta da zaben kwamandan da zai jagoranci mujahidai da tsara rundunar mayaka.
Haka aure wajibi ne, sai dai bawa yana da zabi kan matar da yake so. Haka mace tana da zabi kan miji. Sai namiji ya yi Istihara kan ainihin matar da yake so, haka mace ta yi Istihara kan namijin da take so ta aura.
Sannan ana yin Istihara idan wajibai ko mustahabbai biyu suka bijiro wa mutum a lokaci daya. Sai mutum ya yi Istihara kan wanne ne zai yi, ko wanne ne zai fara yi ko wanne ne zai jinkirta yi.
Misalin bijirowar wajibai biyu shi ne kamar aure da aikin Hajji ga wanda ya mallaki kudin da zai iya yin daya kadai daga cikinsu. Misalin bijirowar mustahabbai biyu kuma shi ne kamar bijirowar jihadi na kifaya da neman ilimi na kifaya ko tare da Hajji na tadawwa’i.
Abin lura: Kada a mance Istihara ta halatta a cikin kowane al’amari da yake halal. Kuma tana kasancewa a cikin abin da yake wajibi da mustahabbi da ake da zabi a cikinsa ko kan wuri ko zamani ko hakikanin wani abu da aka ayyana da kuma inda mustahabbai biyu ko wajibai biyu suka bijiro wa mutum.
Da wannan, maganar Jabir (RA) ta cewa: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana koyar da Istihara a cikin komai...” ta fito fili ke nan.
Ibnu Jamrah ya ce, “(Cewa a cikin kowane al’amari) na nufin bayani ne na gam-hade da ake nufin wasu kebabbun al’amura da shi. Domin wajibi da mustahabbi ba a yin Istihara don aikata su, haram da makaruhi kuma ba a yin Istihara don barin aikata su. Don haka an iyakance yin ta da abin da yake halal ne da kuma mustahabbi idan al’amura biyu suka bijiro wa mutum kan wanda zai fara ko ya takaita a kansa.”
Ibnu Hajrin Al-Askalani ya yi karin bayani kan hakan inda ya ce: “Istihara tana shiga abin da ke bayan wannan da yake wajibi ko mustahabbin da ake da zabi da abin da yake zamaninsa mai yalwa ne ko ya shafi gama-gari, babban al’amari ne ko karami. Domin da yawa karamin al’amari yana iya kunsar manyan al’amura.” (Fat’hul Bari, Mujalladi na 11 shafi na 183).
Ko bawa zai iya sanin sakamakon Istihararsa?
Bayan bawa ya yi Istihararsa kamar yadda shari’a ta nuna, ba wani abu da zai jira sai ya yi azamar yin abin da yake nema ko so, yana mai dogara ga Allah, hakikanin dogaro. “Duk wanda ya dogara ga Allah, to, Shi (Allah) Ya isar masa.” Kuma Ya sake cewa: “Idan ka yi azamar (niyyar) yin wani abu, ka dogara ga Allah, lallai ne Allah Yana son masu tawakkali (dogaro gare Shi).”
Bayan haka, ya kasance mai gaskiyar niyya, mai ikhlasi a cikin al’amari Istiharar. “A lokacin da suka yi azamar (niyyar) yin wani abu da sun gaskata Allah da ya kasance alheri a gare su.” Daga nan ya aikata duk abin da ya bayyana gare shi, ba tare da taraddadi ko bacin rai da damuwa ba, kada ya rika kai-kawo ko jin tsoro, ya-alla abin ya kwanta masa a rai ko bai kwanta ba. Kuma ya-alla kwaciyar ran gabanin Istiharar ce ko bayanta. Domin al’amarin ba wai yana ta’allaka da kwanciyar rai ne ko rashinsa ba, a’a, yana ta’allaka ne da sawwakewar Allah da dacewarSa. Da yawa zuciya takan natsu da wani al’amari, amma ba shi Allah Yake nufi ga bawa ba, kuma ba zai sawwaka masa shi ba ko da ya gabatar da shi a kan saura.
Kuma da yawa zuciya ba ta kwanciya da wani al’amari, amma shi Allah Ya yi nufi ga bawa, Ya kaddara masa shi kuma Ya sawwaka masa shi. Don haka abin da ake fata mutane su gane shi ne:
Na farko: Bawa ya gaskanta Ubangijinsa tare da yakini gare Shi, kuma ya tabbatar da sharuddan karbar Istihara.
Na biyu: Amsar Istiharar bawa daga Ubangiji take.
Idan wadannan sharudda biyu suka cika, kada bawa ya gabatar da batun kwantawar abu a zuciyarsa ko ya kawo rashin kwanta masa a rai. Babu wani mahaluki, ko wane ne shi, da zai hana wani alheri da Allah Ya nufa ya faru gare shi, ko ya kawar masa da wani abin ki da Allah Ya kaddara masa.
Marhalolin Istihara dai su ne himmantuwa ga aikata wani abu, sannan sai yin Sallar Istiharar sai kuma yin shawara sai tawakkali ga Allah, sai kuma mai Istihara ya yi aiki da abin da ya ga ya fi masa.
To yaya batun mafarki a cikin barcin mai Istihara da sauran maganganun da mutane ke fada game da Istiharar?
Kamar yadda ya gabata, kowane al’amari na ta’allaka ne kan sawwakewar Allah Madaukaki da dacewarSa, ba wai da kwantawar lamari a zuciya ko wani abu da mutum zai gani a mafarki ba. Ko wani abu mai kama da haka da bai tabbata daga Sunnar Annabi (SAW) ko wani daga cikin sahabbansa ko manyan malaman Musulunci da ake dogaro da su ba.
Abin da ke kan mai Istihara (shi ne) ya ci gaba da yin abin da ya so, kuma ya sani ba zai iya yin komai ba, sai abin da aka kaddara masa. “Kowa yana tafiya ne zuwa ga abin da aka kaddara masa.” Kuma a sa ma mutum ya yi mafarkin wani abu game da Istiharar da ya yi, to wa ya sani ko wannan mafarki daga Allah yake ko daga Shaidan ko daga zancen zuci? Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafarki kashi uku ne: Ko dai bushara daga Allah; ko zancen zucci; ko tsoratarwa daga Shaidan.” Tirmizi da Ibnu Majah suka ruwaito.
Don haka ko mutum ya yi mafarki ko bai yi ba, mafarki bai gabatar da komai ko ya jinkirtar da komai, kuma Allah Yana kaddara abin da Ya yi nufi ne da abin da Ya so, kamar yadda Ya so.
Zamu chigaba da yardar Allah ....
Salihu Is’hak Makera
Gabatarwa:- Salis kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```