SALLAR ISTIKHARA DA HUKUNCE-HUKUNCEN TA 04

🔹 *ISTIHARA DA HUKUNCE~HUKUNCEN TA* 

*04*

→Dalilin shari’ancin Istihara

Abin da Buhari ya ruwaito a cikin sahihinsa daga Jabir (RA) ya ce: “Manzon Allah ya kasance yana koyar da mu Istihara a cikin kowane al’amari kamar (yadda yake koyar da mu) sura ta Alkur’ani: “Idan dayanku ya himmantu ga aikata wani al’amari, to, ya yi Sallah raka’a biyu da ba na farilla ba, sannan ya ce: “Allahumma inni astakhiruka bi ilimika, wa astakdiruka bi kudiratika, wa as’aluka min fadlikal azim. Fa innaka takdiru wa la akdiru, wa ta’alamu wa la a’alamu wa atna allamul guyub. Allahumma in kunta ta’alamu anna hazal amru – ya ambace shi ko ya fadi abin da yake so- khairul li fi dini wa ma’ashi wa akibatu amri, - ko ya ce:fi ajili amri wa ajilihi- fa kadirhu li wa yassirhu li, summa barikli fihi. Wa in kunta ta’alamu anna hazal amru- ya ambace shi ko ya fadi abin da yake so- sharrun li fi dini wa ma’ashi wa akibatu amri - ko ya ce:fi ajili amri wa ajilihi-fasrifhu anni, wasrifni anhu, wakdirlil khaira haisu kana, summa radini bihi.” (ya ambaci bukatarsa). Buhari mujalladi na 2 shafi na 51.

→Abubuwan da ake Istihara a kansu

 Al’amuran da suke bijiro wa bawa suna tafiya ne tare da hukunce-hukunce biyar. Wato wajibi da mustahabbi da hala da makaruhi da kuma haram.

Wajibi da mustahabbi da makaruhi da haram ba a yin Istihara wajen aikata su ko kin aikata su.

Domin wajibi wajibi ne a aikata shi, haramun ne a bar shi ya alla bawa ya yi Istihara ko bai yi Istihara ba. Haram kumwa haram ne a aikata ta kuma wajibi ne a bar ta, ya alla bawa ya yi Istihara ko bai yi Istihara ba. Kuma ba a yin Istihara kan yi Sallah ko Hajji ko shan giya ko aikata kowane irin sabo ko barinsa. 

To a kan me ake yin Istihara?


Zamu chigaba da yardar Allah ....

Salihu Is’hak Makera
Gabatarwa:- Salis kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```

Post a Comment (0)