SOYAYYA DOMIN ALLAH


SOYAYYA DOMIN ALLAH. 

Imam Ash-Shaukani Allah ya masa rahama yana cewa "watarana na kwana inata kai komo akan hadisin manzon Allah da yake cewa {lalle maso soyayya domin Allah suna kan wasu minbari na haske wanda Annabawa da shahidai zasuso dama ace sune awannan matsayin}, na kasance inata tinani akan wannan hadisin tayaya soyayya domin Allah zata kasance, yaya take da za'ace har Annabawa da shahidai na kwadayin samunta?? 
     Sai nace; hakika dayawa soyayyar da ake samu ayanzu badan Allah akeyinta ba, 
🌹Miiji nason matarsa ba soyayyace domin Allah ba, 
🌹 Mata nason mijinta ba soyayyace dan Allah ba, 
🌺 Ya'ya nason iyayensu ba soyayyace dan Allah ba, 
🌸 Iyaye nason ya'yansu ba soyayyace dan Allah ba. 
    Hakanan; kanason shugaba, dankasuwa, mai wakiltanka, kanason wane saboda kyansa, ko saboda sautinsa, ko saboda kudinsa. 
     Da wannan ne nagane cewa ita soyayya domin Allah ita tafi karanci samada Jan kibreet".

الفتح الرباني مجلد التاسع. 

# zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)