TAMBAYA TA 68


Tambaya
:
Menene hukunci akan Jinin-Al'adar da ya ke yiwa Mace wasa sakamakon ta yi amfani da maganin tsarin iyali??
:
Amsa
:
Alal-Haƙiƙa yin amfani da magungunan hana ɗaukan ciki sukan janyowa Mata wasu matsaloli dabam-dabam, kamar rikicewar al'ada wani lokacin sai Mace taga jinin yazo mata kafin lokacin zuwansa yayi, ko kuma taga yayi jinkirin zuwa a kan lokacinsa, to amma Malamai sunyi saɓani a game da hukuncin jinin da ke fitowa Mace a dalilin amfani da wani magani da ta yi, shin wannan jinin shima jinin-haila ne ko kuma jinin-cuta ne?
:
Wasu daga cikin Malamai sukace Mace za ta duba ne ta gani idan jinin yazo da siffa ne irin ta Jinin-Haila to kawai Jinin-Haila ne, amma idan yazo da wata siffa da ba ta jinin haila ba to ba zai hana ta yin ibadunta ba,
:
Wasu Malaman kuma sukace a'a kawai Mace za ta je ta tambayi Likita ne idan ya ce mata Jinin-Haila ne to shikenan hukuncin Jinin-Haila yahau kanta kenan,
:
Amma wasu Malaman suna ganin cewa dukkan wani jini da zai fitowa Mace a dalilin shan wani magani da ta yi, in dai jini ne sosai sukace to kawai Jinin-Haila ne danhaka za ta saurara ne har ya ɗauke sannan tayi wanka kuma ta ci gaba da ibadarta, amma idan taga Jinin ya wuce kwana (15) bai tsaya ba to kawai za ta yi wanka ne taci gaba da ibadarta, domin hukuncin ya na ratayuwa ne da zuwan Jini ko rashin zuwansa, sukace inda Mace za ta yi amfani dawani magani wanda zai ɗauke mata zuwan Jinin-Haila na tsawon wani lokaci, shikenan tana nan a matsayinta na mai tsarki, babu yadda za a yi hukuncin mai al'ada yahau kanta sai in an ga jini a tare da ita tukuna, to kamar haka kuma idan Mace ta sha wani magani da nufin tsaida Haila ko Tazarar-Haihuwa kuma sai al'adarta ta rikice mata, to duk jinin da yazo mata adalilin haka kawai za a ba shi hukuncin Jinin-Haila ne,
:
Idan kuma ya kasance Misali Mace ta saba duk wata tana yin Jinin-Al'ada na kwana biyar, amma bayan ta yi amfani da maganin Tazarar-Haihuwa sai Al'adar ta rikice mata, to za ta dena Sallah da Azumi har sai wannan jinin ya ɗauke, amma idan ya kasance Jinin da yake zuwa ɗin yawuce kwana 15 kuma bai tsayaba, to kawai za ta yi wanka ne ta ci gaba da ibadarta domin ya zama Jinin-Istahadha, daga nan kuma idan wani watan ya sake dawowa jini yazo mata to hukuncinta za ta koma yin amfani ne da asalin kwanakin da ta saba tana al'ada a cikinsu, idan Misali duk farkon wata ko tsakiyar wata ko kuma karshen wata ta saba tana yin Jinin-Al'ada na kwana 5, to da lokacin yayi kawai zata ware waɗannan kwanaki biyar ɗin da ta saba tana yi, ba za ta yi Sallah da Azumi a cikinsu ba, idan suka wuce sai tayi wanka taci gaba da ibadarta ko da jinin bai tsaya ba,
:
Ko shakka babu wannan magana ta karshe tana da ƙarfi sosai a wajen Malamai,
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)