TA YA YA ZAN GANE NA KYAUTATA..? 🌹
An kar'bo daga Sahabi Abdullah bin Mas'ud (Radhiyallahu anhu) yana cewa, wani mutum ya tambayi Manzon Allah (SAW) cewa : Tayaya zan gane cewa na kyautata ko na munana?? (Ina kyautatawa mutane ko bana kyautata musu)
Sai Manzon Allah (SAW) yace masa "Idan kaji makobtanka suna cewa ka kyautata to tabbas ka kyautata, Amma idan kaji suna cewa ka munana to hakika ka munana".
رواه ابن ماجه وصØØÙ‡ الألباني.
Note:
Dukkan abinda zaka yima wani mai amfani idan ka yi yaji dadi kyautatawa ne.
Mu dage da (ihsani) kyautatawa bayin Allah! Allah Ta'ala yana son masu kyautatawa.
Allah Ta'ala ya kara shiryar damu zuwa ga kyawawan halaye da dabi'u na gari.
# Zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah