*Tambaya:*
Assalamualaikum malam dan Allah ataimaka a amsa min wannnan tambayar aiki aka bamu a makaranta
2: mace mai al'ada ko janaba idan zatayi wanka shin dolene sai ta warware kai ko kuwa ba saita warware ba?
3: Idan kuma ya halatta tayi wanka da kitson wane irin kitsone ya halatta tayi wanka dashi? Shima hadisi ko aya ko kuma wata ingan tattar mgn.
.
*Amsa:*
Waalaiku mussalam
Maganar warware kitso wajan wankan janaba da Haila ga Hadisin Ummu salma nan ina ganin a matsayinki na dalibar ilmi ya ishe ki. Ummu salma ta tambayi manzon Allah saw a kan haka ta ce: “Ya Annabin Allah ni mace ce me yawan gashin kai sena warware in zanyi wankan Janaba da Haila? sai ya ce: *Ai ya wadatar da ke ki watsa ma kanki ruwa sau uku a kan ki sai ki watsa ruwa a jikinki sai ki yi tsarkinki, .......,* to Amma maganar nau'in kitson to wannan sai a kula da kitson da sharia ta amince banda attachment wato alwisaal kenan.
والله اعلم
*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*
*🕌Islamic Post WhatsApp.*