TAMBAYA TA 039


Tambaya
:
Shin ko a na iya fitar da zakka a kan abin da a ke neman kudi da shi, kamar mota ko gidajen haya, da makamantansu??
:
Amsa
:
Addinin Musulunci ya wajabtawa mabiyansa cewa su fitar da zakka a kan waɗansu dukiyoyi da suka mallaka, danhaka zakka tana wajaba a kan tsabar kuɗin da Mutum ya ajjesu a gida ko a banki, ko da kuwa ba juyasu yake ba, kamar misalin wanda yake tara wasu kudi da nufin nan gaba yayi wata buƙatarsa da su kamar sayen gida ko Mota da dai makamantansu, danhaka in dai kuɗin sun kai Nisabi kuma ya shekara to fa dole ne a fitar musu da zakka,
:
Hakanan zakka ta na wajaba akan nau'in dukiyar da a ke juyata ana kasuwanci da ita, kamar mai sana'ar sayen Gidaje, Pulotai, Gonakai, Motoci, Babura Dawakai, Shanu, da dai sauran dukkan wasu kadarori da ake kasuwanci da su, to idan lokacin fidda zakkar mutum yayi za ayi lissafin kuɗaɗen dukkan waɗancan kadarorin sai a hada a fitar musu da zakka, amma dangane da hukuncin fidda zakka a kan abubuwan da a ke yin sana'a ta neman kuɗi da su, wato kamar:
:
(1)-Injin-Niƙa,
(2)-Keken-Ɗinki,
(3)-Gidajen-Haya,
(4)-Motocin-Haya,
(5)-Baburan-Haya,
:
Da sauran dukkan wata Na'ura da a ke yin Sana'a da ita ana samun kuɗi, to asali su dai waɗannan abubuwa komin yawansu babu zakka a kansu, sai dai kuɗaɗen da a ka samu ta hanyarsu idan sunkai nisabi sannan kuma sun shekara a wajen mai su, to wajibi ne a fitar da zakkar waɗannan kuɗaɗen da a ka samu, amma ba za a yi lissafi da asalin kuɗaɗen su waɗannan kayayyakin da a ke yin sana'ar da su ba, sai dai idan yakasance dama Mutum yana Sana'ar saida su kuma yana neman kuɗi dasu, danhaka idan ya samu mai saye to kawai zai sayar ne kuma yaje ya sake sayo wani, to a irin wannan hali idan ya tashi fidda zakka zai haɗa ne yayi lissafi harda asalin kuɗaɗen su waɗannan kayayyakin da a ke yin sana'ar da su ya fitar musu da zakka,
:
Hakanan babu zakka akan dukiya irin ta nau'ikan kayayyakin da Mutum ya tanadesu dan jin daɗin rayuwarsa, kamar kayan alatu da kayan ado da Mutum yake sawa acikin dakinsa ko cikin gidansa, da kuma Motocin hawa komin yawansu, ko kuma Gidaje da Gonakai da Pulotai da Mutum ya mallakesu a matsayin kadara kadai bawai kasuwancinsu yake ba, to dukkan irin wadannan babu zakka akansu,
:
Malamai sun kafa hujja akan rashin bada zakkar waɗannan abubuwa ne da wannan Hadisin na Mαnzon Allah(ﷺ) da ya ke cewa:
:
"ليس علي المسلم في عبده ولا فرسه صدقة"
(رواه البخاري ومسلم)
MA'ANA:
Ba (wajibi bane) akan Musulmi yafitar da zakkar dokinsa (da yake hawa) da Bawansa (da yake masa hidima)
:
Amma Idan zinare ne Mutum yake ajje da shi, to dama shi hukuncinsa kamar hukuncin tsabar Kuɗi ne (Cash), danhaka ƘAULAN WAHIDAN wajibi ne a fitar masa da Zakka, ko da a na juyashi ayi kasuwanci da shi ko ba a juyawa, wato abu in dai sunansa kuɗi kuma ya kai nisabi to fa dole ne idan shekara ta kewayo a fitar masa da zakka, amma dangane da irin zinaren da aka tanadeshi saboda kwalliya na kayan adon Mata, kamar Sarƙa, Ɗankunne, Zobe, Awarwaro, Agogo, dadai sauran kayan ado na Mata irin wanɗanda aka Ƙerasu da Zinare (Gold), Malamai sunyi Saɓani a kansu, Shin suma akwai zakka a kansu ko babu?
:
Mafiya yawa daga cikin Malaman Muslunci sun tafi ne akan cewa babu Zakka akansu, domin suna daga cikin kayan ado na more rayuwa da mai shi take amfani da su, sai dai waɗansu Malaman suna ganin cewa matuƙar dai kayan adon na Zinare (Gold) ne to fa dole ne sai an fitar masu da zakka duk shekara, kuma suma sunkafa hujjarsu ne akan waɗansu dalilai masu ƙarfi da suka dogara akansu, danhaka dai wannan wata Mas'alace da akayi Saɓani akanta, sai dai mafi yawa daga cikin Malamai sunfi rinjayar da maganar cewa babu Zakka akansu
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)