*Abubuwan Da Ake So Miji Ya Fi Matarsa Da Su*
Tambaya : Assalam alaikum, malam da fatan kana lafiya, wasu tambayoyi nake rokon Malam daya taimakamin da amsoshinsu in Allah yasa malam yasansu, shin malam wai akwai wasu abubuwa uku da ake so mace tafi mijin da za ta aura da su,sannan shima akwai abu guda uku da akeso ya fita da su?, sannan akwai wadanda sukayi musharaka akansu, dafatan malam ya sansu, kuma za’a taimakamin da su.nagode
Amsa :
Wa alaikum assalam.To dan’unwa masana ilimin zamantakewar aure suna cewa, ana so mace ta fi mijinta da abubuwa uku : ta fi shi a kyau, ta fi shi kananan shekaru, ta fi son shi, sama da yadda yake sonta . Ana so miji ya fi matarsa da abubuwa uku : ya fi ta kudi, ya fi ta ilimi, ya fi ta jarunta. Ana so su hadu a abubuwa uku : ya zama akwai yaran da yake hada su, ya zama addininsu daya, ya zama dukkansu suna son tarbiyya. Idan aka samu wadannan uku-ukun, to za’a samu jin dadin aure
Allah ne mafi sani
Dr, Jamil Yusuf zarewa
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```