*Tambaya:*
Assalamu alaikum!
An tashi lfy ya family and studies?
Malam Allah kara maku basira da hakuri da mu. Amin
Tambaye ta ita ce.
Malam mutum ne yayi aure sai mijin ya fada ma matan cewa shi bai san haihuwa saboda tarbiyan yara yanzu yayi wuya, shi ya ya kare da nashi zunubin balle na yara. Shi bai san me zai fada ma Allah ba idan ya kawo su duniya kuma suka lalace, zinace zinace, shaye shaye da sauran su. Shi ne ya fada mata amma idan taga tana so toh ta shirya abun da zata fada ma Allah dun Shi ba ruwan shi. Toh malam hakan akwai kuskure ko ya fadi dai dai dun Allah a amsa mana dun musan gaskiya lamarin.
.
*Amsa:*
WA'alaikumussalamu.
Wannan yana cikin abin da jahiliyya suka tsorata wajan kin *'ya'ya* musamman 'ya mace saboda abin kunyar da suke yi galibinsu, to waccan ita ce jahiliyyar farko su ma 'yan jahiliyyar karshe sun zo da tasu amma in ka duba sosai sai ka taras kawai ba don abin da iyayen za su fuskanta bane gaban Allah a'a kawai saboda dawainiya ne in ba haka ba iyaye abin da aka dora masu shine tarbiyya amma shiriyar yaran tana hannun Allah kamar yadda Annabi Ibrahim AS mahaifin shi ba zai cutar da shi ba duk da ba musulmi bane, haka Annabi Nuh ďansa bai bi shi ba kuma Allah be tuhunce shi ba a kan hakan.
Saboda haka wannan mijin bai da hurumi a shari'a wajen rashin son haihuwa, ra'ayin marasa sanin Addinin Allah ne kawai in shi shiryayye ne shi ya ya shirya kansa kuma iyaye ba su ba shi gudunmawa ba? haka kawai ya zama? Mu yadda mu bayin Allah ne ba za mu yi komai ba sai yadda yake so a bisa koyarwar Annabinsa SAW kuma Allah Ya fi kowa sanin lokaci irin haka zai zo amma be ce kar
a haihuba duk da ya saukar da dokar da duniya za ta bi tun farkonta zuwa karshenta.
cikakken bayani aduba
*التقصير فى تربية الاولاد*
_*الشيخ محمد ابراهيم الحمد.*_
والله اعلم.
*Barr. Ukashatu Abubakar Giwa.*
*🕌Islamic Post WhatsApp.*