TAMBAYA TA 67


*SHIN KO SHARI'A TA YADDA MUTUN YA KAURACEWA MATAR SA DA SUN SAMU SABANI YA BARTA BA ABINCI BA KWANA A DAKIN TA?*

*Tambaya*

Assalam alykum warahmatullah Mlm ina da makwafciya su biyu ne wajen mijin to da abu yafaru tsakaninsu matan da mijin wdd sukayi rashin jituwar sai yabar dakinta yakoma dakin dayar tace ko kwanan tane bazai shiga ba Mlm tace sai yayi fin sati adaki daya baya kulata bare kudin abinci Mlm haka dayake ya dace da shariar Ubangiji Allah ngd

*Amsa*
Wa'alaykumussalam

Haka ba dai dai bane, domin shari'a ta zo da tsayar da adalci...
Tayi kokarin tattaunawa dashi cikin lumana don tina masa hakin ta dake kan sa idan ya gyara toh shikenan idan kuma bai gyara ba toh sai ta kai shi gaba (sanar da magabatan sa) domin suyi masa nasiha.

Wallahu A'alam

*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

05/04/2020

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Post a Comment (0)