YADDA AKE HAƊA PEANUT BOGGER

RAHMAT KITCHEN & MAKE UP 🍝🌶💄👄 
    
    PEANUT BOGGAR
    
      Ingredient

* gyada
* kwai
* sugar
* milk
* fulawa 
* baking powder
* gishiri 
* mai
 
     METHOD

Zaki sami gyadan ki ki tsinceta ki wankata sannan ki bazata a rana ta bushe bayan ta bushe zaki soya ta kadan ita bata soyu ba kuma ita ba danya ba bayan kin gama se ki dakko kayan hadinki , zaki fasa kwan ki a wuri mai kyau se ki saka sugar acikin ruwan kwan ki zaki yi ta buga shi har se sugar ta narke bayan ta narke se ki dakko madara na gari amma ki zuba akai se ki kara baga shi har su hade jikin su in kika gama se ki dakko fulawan ki da ki ka Riga kika tankade ta se ki saka baking powder dinki da gishiri kadan seki jijjuya su su hade jikin su bayan kin gama se ki dakko gyadar ki se ki zuba hadin ruwan kwan ki kadan se ki jijjuya ta ko ina ya ji bayan kin gama juyawa se ki dakko hadin fulawar ki kina zubawa kina jiwa da sauri-sauri Dan kar ta cure wuri daya in in fulawar taji ko ina se ki kara zuba hadin ruwan kwanki ki kara jiyawa se kuma kara dakko hadin fulawar kira zuba kaman yadda kikayi a farko se ki Dora mai a wuta amma kar ki saka wuta da yawa idan manki ya dakko zafi se ki saka idan ya soyu zaki ga yayi kamar cin cin amma kar ki bari yayi duhu sosai.🥜

 Wannan hadin za'a iya Bawa yara ma suci ba shida zaki sosai kuma zai kara musu lafiya ajiki .💃

   By
 Maman Hafsat 
      (Mrs Ismai'l)❣

Post a Comment (0)