ZAGIN MATACCE


ZAGIN MATACCE....

IKRAMA BIN ABI JAHIL ya nuna qiyayya Mai tsanani ga addinin islama bayan yaqin uhud ya na cikin y'an committee da aka kashewa iyayan su a yaqin uhud, don HAKA ya cutar da muslunci matuqar cutarwa

HAKA Nan Abu ne bayyananne a tarihin muslunci irin cutarwar da Abu jahil yayi wa Annabi Sallallahu alaihi wasallam

Bayan fatahu makka Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace game da mutanen makka duk Wanda ya shiga ka'aba ko gidan Abu Sufyan ya tsira, Amma yace duk inda IKRAMA BIN ABI JAHIL ya shiga a kamo shi a kashe shi, da IKRAMA yaji labarin ya gudu ya bar garin can ya kusa tsallaka gabar kogi, matar IKRAMA BIN ABI JAHIL ta karbi muslunci taje ta roqi Annabi ya yafewa IKRAMA, Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya yafe Masa, 
Sannan matar sa ta bi bayan sa ta sanar dashi cewa Annabi ya yafe masa, ya dawo zuwa garin makka ya muslunta 
Kafin ya dawo Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace da sahabban sa
"IKRAMA ZAI ZO MUKU YANA MUMINI MAI HIJRA , KADA KU ZAGI BABAN SA, DOMIN HAQIQA ZAGIN MATACCE YANA CUTAR DA RAYAYYE BA YA ISA GA MAMACI"

TO KAI A MATSAYIN Ka NA MUSULMI MAI IKRARIN BIN KOYARWAR ANNABI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM A INA KA SAMO NAKA ILIMIN NA ZAGIN MAMACI? 

na tabbata duk irin yadda kake Jin cewa bawan Allahn ya cutar da Kai ( idan ma ya cutar da Kai din) ba najin zai Kai 1/10 na cutarwar da Abu jahil yayi wa Annabi Sallallahu alaihi wasallam, Amma Habibiy abin koyin mu sallallahu alaihi wasallam yace kar a ZAGe shi!!!

Don HAKA idan ka zagi margayi Abba kyari don kana rayawa ya zalunce ka to ZAGIN ka ba zai Isa gare shi ba, sai dai in iyalin sa da masoyan sa sun ji ZAGIN ya cutar dasu Wanda su Kuma Basu mulke ka ba ballantan su zalunce ka, ka ga anan Kai kayi zaluncin 

Ya kamata mu zama masu aiki da hankali da Kuma ilimi

Allah ya gafarta Masa yasa aljanna ce makomar sa ya kyautata namu qarshen

✍️ Hauwa Tijjani Musa
Post a Comment (0)