*WATAN SHA'ABAN*
✍🏽 Rubutawa: *Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa (Hafizahullah).*
Taken Hudhuba Yau
wannan wata shine wata na takwas a kalandar musulunci, yana tsakanin Rajab da Ramadan.
Asalin sunan wannan wata ya samo asali daga tarwatsewa ko rarrabuwa, domin Larabawa suna tafiya neman ruwa, a cikin watan wata, ko kuma suna yawan kai hare hare ga juna a cikin wannan watan shi yasa aka kira shi da suna Sha'aban, Ibn Hajar Fathul Bari. 4/213.
2. Falalar watan Sha'aban. Usamatu Ɗan Zaidu ya tambayi Manzon Allah saw yace : ya Rasulallah Banga kana yin azumi a cikin wani wata ba kamar yadda ka ke yi a cikin wannan watan? Sai yace wannan wata ne da mutane suke shagala a cikin sa saboda yana tsakanin Rajab da Ramadan, kuma a cikin sa ake ɗaga Aiyukan bayi zuwa sama, don haka nake son a ɗaga aiyuka na ina azumi, Albani ya Hassana shi.
3. Yawan azumin nafila a cikin wannan wata, saboda hadisan Nana Aisha tace:Manzon Allah saw, baya yin wata guda yana azumi inba a watan Ramadan ba, kuma babu wani wata da Annabi saw yake azumin nafila a cikin sa da yawa kamar watan Sha'aban. Bukhari.
4. Ana gafarta zunubai a cikin wannan wata, Manzon Allah saw yace :lallai haƙiƙa Allah ta'ala yana Tsinkaya a cikin daren sha biyar ga watan Sha'aban, yana gafara ga dukkan bayinsa sai masu shirka kawai ko kuma masu gaba da juna, Ibn Majah.
5. Hikmar da ya sa ake son yawan azumi a cikin watan Sha'aban, saboda a saba da azumin kafin shigowar Ramadan, domin jiki ya saba, a shiga cikin Ramadan da nishaɗi, kamar yadda Ibn Rajab ya faɗa.
6. Wannan watan yawan karatun Alkur'ani mai girma ne, saboda magabata suna shagala da yawan karatun Alkur'ani mai girma a wannan wata, kamar yadda Ibn Rajab ya ruwaito a cikin liffafin Laɗa'iful ma'arif.
7. Ba a keɓance daran sha biyar kawai da salla ko azumi, domin hadisan da suka zo da haka basu inganta ba.
Mu shagala da lbada da zikiri, da istigfari da salatin Annabi saw, da yawan Sadaƙa.
Allah ya kaimu Ramadan, ya kuma yaye mana dukkan damuwa.