HALIN DA MU KE CIKI A YANZU


Halin da muke ciki a yanzu shine
.
Malamai suna ta iya kokarin su wajen ganin sun wayar wa al'umma da kai, amma kuma a gefe guda an samu wasu sashi acikin jahilai da miyagun malamai masu son zuciya suna kokari wajen batar da Al'umma, Allah ya tsare mu
.
Wajibi ne 'yan uwa mu tashi muyi karatu domin kare martaban mu da mutuncin mu domin neman mafaka a wajen Allah
.
Kada son zuciya da makauniyar soyayya ga malamai ta sanya mu muyi watsi da hanyar salaf, aqida ta salaf aqida ce tattacciya wacce babu komai akan ta sai gaskiya da kuma son gaskiya da kuma bin gaskiya kada muyi wasa da daman mu yaku 'yan uwa
.
Kuyi hakuri wajen yiwa shuwagabanni biyayya kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya jaddada wannan umarni ga mabiyan sa, Allah ya datar damu
.
Ustaz Hussaini Haruna Kuriga
Post a Comment (0)