AZUMIN MAI HAILA DA BIƘI


AZUMIN MAI HAILA DA MAI BIƘI

Baya halatta ga mai jinin haila ko na biƙi(haihuwa) ta yi azumi qaulan wahidan, sannan koda ta yi azumin bai yi ba, idan kuwa da gangan ne tayi to dole ta tuba ga Allaah SWT.

Abunda ke kan mai haila ko jinin biƙi in sun sha azumi shine ramuwa.

GA WASU TSOKACI:

A) BAMBANCI TSAKANIN JININ HAILA DANA ISTIHADA(CUTA):
1. Jinin haila yana da duhu wanda yake karkata zuwa ga ruwan ƙasa-ƙasa ko kunkunniya. Shi kuwa jinin istihada sakakke ne mai karkata zuwa ga haske.
2. Jinin haila yana da wari ko ƙarni.
3. Jinin haila yana tunkuɗa yayin fitowar sa, saɓanin na istihada wanda shi bai fiya tunkuɗa ba.
4. Mafi yawan lokuta kafin da kuma lokacin zubar jinin haila akan ji zafi ko ciwo a māra ko kwankwaso ko ciki.

B) ALAMOMIN TSARKI BIYU NE:
1. Zuba ko fitowar farin ruwa wanda mahaifa ke tunkuɗo shi waje bayan jinin haila ya gama zuba.
2. Bushewar gaba(farji), wato ɗaukewa ko yankewar jinin, wanda wasu lokuta akan tabbatar da haka ne idan an saka kyalle a cikin farji, sannan aka cire shi a bushe bayan ɗan lokaci ba tareda jini ba. 

C) SANNAN Ga wani takaitaccen bayani wanda ɗan'uwa malam Abu Uwaisat Zaria ya taɓa yi wanda zai taimakawa mata wurin tantance rikicewar jinin haila da na cuta da kuma tsarki:

1. Ta kiyaye irin launin jinin da ke zuwan ma ta cikin kwanakin hailar ta. 

2. Ta kiyaye yanayin wari ko ƙarnin jinin ta a lokacin al'ada. 

3. Ta kiyaye alamar tsarkin ta. 

Idan ki ka ga tsarkin ki bayan kwanakin hailar ki sun cika, sai kuma wani jinin yazo a cikin wannan watan mai irin launi da ƙarnin jinin hailar ki, sai ki kuma bashi hukuncin jinin haila, a ƙarƙashin haka sai ki sake barin ibadoji har sai kin tsarkaka. Idan kuwa ba shi da waɗannan siffofin to ya zama jinin istihādah(wato jinin ciwo ko rauni), wanda shi baya hana ibada ko mu'amalar aure, sai dai a nema masa magani wurin likitoci.

Dan haka, akan iya yin jinin haila sau biyu ko sau uku ko makamancin haka a wata daya. 

Allaah Yasa mu dace.

Abdullahi Almadeeniy Kagarko.
28/Ramadan/1441
21st May, 2020
Post a Comment (0)