*ZA'A IYA FITARWA DA KIRISTA ZAKKAR FIDDA KAI ??*
*Tambaya*
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Ina yiwa mlm fatan alkhairi, Allah ya kara budi. Wasune suke neman fatawan akan wnn mas'alar "musulmine yake auren Christian, to wai idan zai fidda zakkar fidda kai itama zai fitar mata?"
*Amsa*
Wa alaikum assalam
Hadisi ya tabbata daga Ibnu Umar cewa: "Annabi (SAW) ya farlanta zakkar fiddakai akan kowanne musulmi Da ne ko bawa" kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.
Hadisin da ya gabata yana nuna musulmi ake fitarwa zakkar fiddakai, amma kafiri ba'a fitar masa, kuma ba'a shi in an fitar.
Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
07/06/2018