TSAKANIN MU DUK DA BANBANCINMU 29


*⚖️TSAKANIMMU DUK DA BAMBANCIMMU//29 NA QARSHE 📿*


*GINSHIQI NA 29*

*Rubutawa: Baban Manar Alqasim*

KOWA YA YI ADDININSA

A zahiri sanya wa wani ido a kan lamuransa kauce wa hanya ne kuma addin muslunci bai zo da haka ba, sai in abinda ya shafi sakin hanya to dole shari'a ta shigo ciki, addini ba na kowa ne ba na Allah ne, kuma dole kowa ya yi shi kamar yadda aka aiko shi, da mutum zai kafurce haka yake so, amma shari'a ba ta ba da hurumin a zuba masa ido ba don ba an halitto shi ya yi abinda ya ga dama ne ba, banda haqqoqin Allah a kansa akwai na mutane.

Shi ma yana haqqi dole a kan makusanta da sauran 'yan uwa musulmi da shugabanni a addini dole kowa ya sauke haqqinsa, in ya yi zina sha'awarsa ce da zabinsa da zabin wace ya yi da ita, amma akwai haqqin addini dole a yi masa ko a yi musu haddi, haka sauran ababan haramci, mutum bai isa ya yi su bayan haramci kuma a zuba masa ido ba, don duk abinda ka ga an haramta sai ka ga illarsa a kan mai aikatawan ko a kan waninsa ko matattarar da yake, shi ya sa ma Allah SW ya riqa turo manzanni don su riqa seta al'umma suna saka su a layi, ba don haka ba da sai a bar kowa ya yi abinda ya ga dama.

Tunda Annabi SAW ya zo shikeban ba sauran wani manzo kuma sun yanke sai malamai, wadannan malaman su ne za su gaji annabawan kamar yadda Annabi SAW ya ce "Malamai magada Annabawa ne, haqiqa Annabawa ba su bar gadon Dinare da Dirhami ba, sun bar ilimi ne, wanda ya samu ya yi babban rabo (Al-Albani ya ciro shi a Sahihul Jami 6297) malamai ne yanzu masu tunatarwa, alal aqalla za a ga wasu sifofi na natsuwa tare da su, kamar kame baki da sauran gabobi, mu kam al'ummar Annabi SAW mun fi sauran al'umman da suka gabata ne saboda wannan gado da aka bar mana, Allah SW ya ce ((Ku ne mafifitan al'umma ga mutane kuna yin umurni da abu mai kyau kuna hana mummuna kuma kuna yin imani da Allah)) Ali-Imran 110.

Sharadin anan bayan imani da Allah akwai umurni da abu mai kyau da hani da mummunan aiki, za mu gani qarara yadda Allah SW ya tsine wa Banu Isra'ila ya ce ((An la'anci wadanda suka kafurta cikin Banu Isra'ila a harshen Dauda da Isa dan Maryam saboda sabonsu da wuce gona da iri • Ba sa hanuwa a kan wani mummunan aiki yin abinsu suke yi, tir da abinda suka riqa aikatawa)) Al-Ma'ida 78-79, idan malamansu suka ja kennensu kan abinda suke yi suka qi bari sai su fita harkarsu, daga baya su zauna a cikinsu su ci gaba da aikatawa tare, ga sakamakonnan an tsine musu gaba daya.

Annabi SAW ya ja wa jama'arsa kunne inda ya ce a hadisin Nu'uman bn Bashir ya ce "Misalin mai tsayawa kan iyakokin Allah da mai abkawa ciki kamar mutane ne da suka hau jirgi (mai hawa biyu), wasu suka hau gidan sama, wasu kuma suna gidan qasa, to idan na gidan qasan suna jin qishi sai su leqo saman su ce "Da za mu fasa jirgin ta qasa daidai da inda muke ba za mu matsa muku ba" to idan na saman suka qyale su su je su yi abinda suke so za su mace gaba daya (don jirgin zai nutse in aka fasa), in suka kame su suka hana su aikatawa za su tsira gaba daya (Buhari 3/139, 2493) kenan mutum bai iya cewa kowa tasa tafisshe shi, ya je ya yi abinda yake so.

Domin sakamakon in ya tashi zuwa kowa zai shafa, shi ya sa ma Allah SW yake cewa ((Ku ji tsoron fitina, haqiqa ba wadanda suka zalunci kansu kadai za ta shafa ba)) Al-Anfal 25, duk in aka sami mutane a cikin laifi a yi qoqarin fitar da su ba wai a gaya wa duniya su san cewa wane fa mabarnaci ne ba, kar wannan ya zama shi ne burin mai kira zuwa ga Allah, kuma kar ya kasance an gaya masa laifin kawai an qyale shi, a'a, a taimaka masa ta hanyar da ta dace wace za ta ja shi zuwa ga tsira.

Malamai na qoqarinsu iya iyawansu, galibin matsalolin duk a tsakankaninmu ne dalibai, in sun fadi magana da wata siga ta koyarwa sai mu dauka mu je mu yi ta tattauna ta a qarshe mu ce ga abinda malam wane ya ce, kuma yana yi ne da wane, in ba a yi sa'a ba sai a dauki maganar a kai masa, sai ka ga wata wutar ta kunnu, Allah ya yi mana maganin abinda zai dame mu ya shiryar da mu hanya madaidaiciya ya kiyashe mu aikin da-na-sani, idan yin wa'azi haqqin malamai ne gyaran kuskure dai yana kan kowa.

A hadisin Abu-Sa'id Al-Khuduri RA yana cewa na ji manzon Allah SW yana cewa "In dayanku ya ga kuskure to ya gyara da hannunsa, idan kuma ba zai iya (da hannun) ba to (ya gyra) da harshensa, in kuma ba zai iya (da harshen) ba to (ya gyara) da zuciyarsa, wannan ne mafi raunin imani (Muslim), duka sauran hanyoyin gyaran imani ne na qarshe ne mafi rauni a ciki, alal aqalla in mutum ya kasa sa hannu ya gyara, ya kasa yi wa wani fada a qarshe dai ya hana kansa ya yi qoqari, mu dai abinda za mu iya yi kenan mu rubuta, wata qila wani ya ga abinda zai amfane shi ya dauka.

Sai dai ina yi mana kyakkyawar zato, duk abinda aka yi shi domin Allah to Allan zai sanya masa albarka, a hadisan Sahal bn Sa'ad Annabi SAW yake ce wa Aliy RA "Rantsuwar Allah kenan, Allah ya shiryar da mutum guda a dalilinka ya fi a ba ka jajayen raquma (Buhari da Muslim), mu yi haquri da mutane, mu kuma girmama malamanmu, duk al'ummar da qanananta ba su dauki manyanta a bakin komai ba bayan kuma manyan su ne masu shiryarwan haqiqa ta fada halaka, malamai su san darajar shugabanni su yi kira a girmama su, dalibai su san darajar malamai koda fahimta ba ta zo daya ba, Allah ya sada mu a shiri na gaba.

Allah ya amsa mana ibadun mu.

A biyo mu gaba da wani sabon darasin.

*Gabatarwa: Abulfawzhaan*

*Follow my Facebook Page*
https://www.facebook.com/100625758324355?referrer=whatsapp
Post a Comment (0)