WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI 4


WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI

Kabir Abubakar Asgar

Fitowa ta Hudu

C. TARIHI BA SHI DA KARA

A dabi’ar dan adam akwai daga-kafa da kawaici da rufa-rufa da naka-sai-naka. Sai kuma, uwa-uba, tsabagen son kai. Kowa bai son a taba shi ko a taba na kusa da shi, amma shi zai taba wanda ya so tabawa. Kamar dai yadda bahaushe ke cewa: ‘wanzami ba ya son jarfa’. 

A qoqarin masana tarihi na fitar da shi daga cikin rukunin ‘fannoni’ da kuma tsunduma shi cikin tawagar ‘kimiyya’ tsantsa sun gindaya sharudda da yawa. Muhimmi cikin wadannan sharuddan akwai batun ba-sani-ba-sabo. Abin nufi shine, a wajen rubuta tarihi dole ne tantance maganganu a kuma tabbatar da sahihancinsu sannan a zayyana kuma a siffanta komai yadda ya faru a tarihance ba tare da tunanin cewa a garin yin haka za a dadada wa wani ko a ci mutuncin wani ko wasu ba. 

A dalilin haka ne masana suke ayyana wasu marubuta da suka gaza wajen mu’amalantar tarihi a matsayin ‘kimiyya’. Daga cikin wadanda zan iya tunawa anan akwai Abu Abdullahi Ibn Najjar da Abul Muzaffar Ibnun Jauziy da kuma Abu Shamah. Wadanna masana, sau da dama, Zahabiy ya kan yi nuni izuwa ga gazawa ko zagewar su wajen hakaito labarai. A baya-bayan nan kuma akwai irin su Suyutiy musamman a cikin Tarikhul Khulafa’i.

A ‘yan shekarun baya, lokacin da Isma’il Tsiga yai juya jerangiyar ‘interviews’ din da yai wa Abubakar Mahmud Gummi zuwa littafin da aka fi sani da ‘Manufata’ ko ‘Where I stand’ a turance, an ce wasu mutane sun ta fadi-tashin ganin an hana bugawa da yada littafin, saboda a cewarsu, a cikin tattaunawar Abubakar Gummi ya ambaci sunayensu kuma ya bayyana irin yadda suka dinga qoqarin tadiye shi da kawo wa da’awarsa cikas.

Tare da cewa, wasu malamai sun yi iyakar yin su wajen tsage gaskiya, amma Allah cikin ikonsa, bai qaddara wani littafi ya zamo da cikakken inganci ba kamar yaadda Shafi’iy yake cewa. Sakamakon haka, Alqur’ani mai girma shine kawai littafin da labarai da sauran maganganun da ke cikinsa suka siffantu da inganci dari-bisa-dari.

(To be continued)
Post a Comment (0)