*💔DAMAN ASHE HAKA SO YAKE?? 💔*
*LABARIN WATA YARINYA*🕊
💔Acikin goma a kwashe uku, zai zama daidai da bakwai (10-3=7), shekaru bakwai, shekaru bakwai kenan na kasance ina cikin soyayya tare da wani mutum. Abun kamar jiya ya faru kuma har yanzu ina tunanin shi. Ina tuna lokacin farko da na fara jin muryarsa mai dadi acikin kunnuwana daga gefen wayar da muke yi dashi. Tattaunawarmu ta fara ne daga "Assalamualaikum. Wa ke magana? Don Allah " yi haƙuri .... amman lambar ba daidai bace (wrong number)! "Ee, abu kamar wasa - sai muka fara samun fahimtar juna.
💔Magana ta mintina uku kacal ta dore a matsayin abokantaka, bana yin wata magana mai tsayi dashi amma yakan bani mamaki a duk lokacin da ya ce dani - *"yana ƙaunata."* Na kan tambaye shi shin yayi hauka ne? haka kawai zai fara son mutum ba tare da ya ga fuskarsa ba ko ya taba haduwa dashi ba? Yakan gayamin cewa ya ga zuciyata tana da kirki da tsabta shiyasa yake kuma so na. Amma Ban sani ba shin abinda ya fada gaskiya ne ko kuma yana yi min gatse ne kawai da wasa zuciyata don ya shaho kai na. Kai na takaita muku labari atakaice tun yana kirana ina ce masa wrong number a haka har muka saba dashi na amince masa. Ana haka ya baro garinsu wata rana don ya hadu da ni. Ina zaune a kan kujera a wani wurin shakatawa sanye da baƙin burkha (wato hijjabi) da niqabi. Jikina yana ta rawa, saboda farkon haduwar mu dashi kenan.
💔Ahh ya kira ni sau da yawa yana tambayata- 'A dai dai Ina nake? Me yasa bana iya ganinki? Ni kuma nakan mayar masa da tambayarsa da cewa- "kana daga wane wajene? Wane irin kaya ka saka?" Can sai na hangi wani mutum daga nesa mai tsayi inci 6 yana da dan tsayi, kyakkyawa yana kallon nan da can (da alama yana neman wani), yana tafiya yaje ya dawo, Na buga lambarsa don in gani ko shine mutumin da nake jira naga zai dauki wayarsa ko a'a? - don na share shakku da tantama, ai kuwa sai ya dauka.
💔Daga karshe dai na hadu dashi, mun dauki lokaci mai tsaho dashi, muka ci abinci, amma duk tsawon wannan lokacin iya idona kawai yake gani (saboda niqabin dake fuskata). Kafin mu yiwa juna sallama, sai ya tambayeni cikin nutsuwa - shin ba zan iya samun alfarma na ga masoyiyar tawa ba? Sai na cire niqabi na, shi kuma tare da wani murmushin jin dadi sannan ya ce - "Ma sha Allah - kina da kyau fiye da yadda nayi tunani". A haka muka rabu.
💔Ana haka shekaru suka shude. Har ya kammala collage ya samu shiga jami'a amma abin baƙin cikin shine, dole ne ya bar karatunsa a tsakiya ba don komai ba saboda yana fuskantar matsaloli da wahala a rayuwarsa, dayake shine ɗan fari a wajen iyayensa, yana da nauyi a wuyansa da yawa saboda mahaifinsa ya mutu kuma dole ne ya ɗauki hakkinsa na kula da yan uwansa. Yakan yawan fadamin damuwarsa da matsalolinsa ni kuma na kanyi kokari wajen rarrashinsa da bashi haquri.
_•••> Zamu cigaba a fitowa ta biyu.... ✍️_
✍Rubutawa: *Yar uwarku Muhazzabin*
📝Fassarawa: *Abdullah A Abdullah Abou Khadeejat Assalafeey (أنصار السنة)*
03/04/2020
Gabatarwa:- *Abu Abdurrahman Ahmad Umar Rimi Assalafeey (Assalafeey Rimi)*
*A ZAUREN MACEN KWARAI*
*• Ga masu buqatar shiga Zauren MACEN KWARAI sai a turo da cikakkiyar sallama tare da Cikakken suna da Address ta wadannan Numbobi kamar haka:- +2348036692586 a whatsapp.*