DAREN LAILATUL QADRI


DAREN LAILATUL QADRI !

ALLAH Yace'';
( إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ )

القدر (1) Al-Qadr

Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul qadri 
Manzon ALLAH ﷺ Yace'; Duk wanda yayi tsayuwar daren lailatul qadri, yana mai imani da neman lada a wurin ALLAH, ALLAH zai gafarta mishi abunda ya gabata na daga zunuban sa.  
Bukhari 1901' Muslim 760
Daga A'isha uwar muminai (RTA) tace'; Manzon ALLAH ﷺ Ya kasance yana kokari cikin goman karshen watan RAMADAN, irin kokarin nan da ba yayi a wani watan da ba shi ba. Saheehul Muslim 1175
Manzon ALLAH ﷺ Yace'; Ku nemi daren lailatul qadri a cikin goman karshen watan RAMADAN. 
Saheehut tirmidhi 792
Daga A'isha uwar muminai tace'; Manzon ALLAH ﷺ Ya kasance idan goman karshen watan RAMADAN ya shigo yana kara zage dantse, yana raya daren sa, kuma yana tayar da iyalan sa. 
Saheehul Muslim 1079
Manzon ALLAH ﷺ Yace'; Ku nemi daren lailatul qadri, a cikin witri (wato 21, 23, 25, 27, 29) na goman karshen watan RAMADAN. Bukhari
Daga Ibnu Umar (RTA) Yace'; Lallai wasu mazaje cikin Sahabban Manzon ALLAH ﷺ an nuna musu lailatul qadri a bakwai din goman karshen watan RAMADAN (daren 27 na watan RAMADAN), sai Manzon ALLAH yace ni ina ganin abinda kuka gani ya jerantu a bakwai din goman karshen watan RAMADAN (daren 27 na watan RAMADAN) duk wanda yake so ya riske ta, to yayi ta kokarin neman ta a bakwai din karshen goman watan RAMADAN (daren 27 na watan RAMADAN). Bukhari da Muslim suka ruwaito
Daga A'isha uwar muminai (RTA) tace'; ta faɗi wa manzon ALLAH ﷺ shin kana ganin idan nayi tsayuwar daren lailatul qadri wani addu'a zan dunga yi? Sai Manzon ALLAH ﷺ Yace da ita ki runga cewa'; 
((اللَّهُمَّ إنَّكَ عَفُوٌ تُحِبُّ العَفْوَ فَاعْفُ عَنّي))
 ALLAHUMMA INNAKA AFUUWUN TUHIBBUL AFWA, FAAFU ANNA.
Saheeh Ibnu Majah 3119

✍🏽 Rasheedah Bintu Abeebakar
(Daughter of Islam)
Post a Comment (0)