Sanya mutane Dariya ta hanyar basu labarai.
Irin wannan labaran yana da hali guda biyu zuwa uku:
1- Idan labari ne na ban Dariya kuma gskia ne, sannan ya kubuta daga cin mutuncin wani ko isgilanci gare shi to wannan ya halasta kai tsaye.
2- Idan labari ne na ban Dariya da aka samo shi wanda ba a da yakini akan gskiyar labarin to babu laifi kaima ka bada wannan labarin ga mutane don suyi Dariya, sai dai bai kamata a lazimci yin hakan ba sbd abinda yake haifarwa na kekashewar zuciya da yawan Dariya da bata lokaci akan abinda baya da wani muhimmanci sosai maimakon ambaton Allah Madaukaki, barin bada irin wannan labarin shiyafi zamowa Alkhairi akan bada labarin.
2- Idan kuma labarin ban Dariya din karya ne da aka kirkira to wannan haramun ne domin ba a shigar da farin ciki zukatan mutane da labaran karya, kai akwai narkon azaba ma ga wanda yake yin hakan bai tuba.
Malamai suna cewa Tirmizi ya ruwaito cikin Sunan hadisi na 2,315, da Abu Dawud hadisi na 4,990 cewa Manzon Allah mai tsira da Aminci yace:
ويل للذى يحدث فيكذب ليضحك به القوم، ويل له ويل له.
Bone ya tabbata ga wanda yake yin zance sai ya kirkiri labarin karya domin ya sanya mutane Dariya da shi, Bone ya tabbata a gare shi, Bone ya tabbata a gare shi.
Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah yake cewa:
ففاعل ذلك – أي : مضحك القوم بالكذب - مستحق للعقوبة الشرعية.
"مجموع الفتاوى " ( 32 / 256 ) .
Me aikata hakan, abin nufi me sanya mutane Dariya da labaran karya ya cancanci ukuba na shari'ah.
Don haka irin yadda ake yada labaran ban Dariya na karya a Whatsapp da wasu shafuka a Facebook don nishadantarwa duka wannan yana daga cikin Manyan zunubai da Allah Madaukaki cikin Nisa'i Ayah ta 31 yace:
إِن تَجْتَنِبُوٱ كَبَآئِرَ مَا تُنْهَوْنَ عَنْهُ نُكَفِّرْ عَنكُمْ سَيِّئَاتِكُمْ وَنُدْخِلْكُم مُّدْخَلًا كَرِيمًا*
Idan kuka nesanci kaba'ira da aka haneku aikata su zamu kankare muku munanan laifukanku kuma zamu shigar daku wani mashiga na karimci.
