FALALA DA DARAJOJIN ALQUR'ANI


FALALA DA DARAJOJIN AL- QUR'ANI.

1- Qur'ani maganar Allaah ne SWT, dan haka shine mafi kyawun zance.
2- Qur'ani zai ceci wadannda ke karantashi kuma suna aiki dashi.
3- Duk harafi É—aya da mutum zai karanta za a bashi lada goma, sannan Allaah zai ninka mishi wannan ladan zuwa adadi mai yawa.
4- Ma'abota Qur'ani sune nakusa da Allaah SWT.
5- Mala'iku suna halartar duk wani wuri da ake karanta Qur'ani ko ake wani darasi da yake da alaka dashi.
6- Rahma da nutsuwa suna sauka kan masu karanta Qur'ani.
7- Mala'ikun rahma suna tare da ma'abota Qur'ani.
8- Duk wanda ya koyi Qur'ani kuma ya koyar dashi to shine mafificin bawa a wurin Allaah SWT.
9- Iyayen ma'abocin Qur'ani za a yi musu kambi na girmamawa a ranar alƙiyama, a karshe kuma a shigar dasu Aljannah.
10- Gwargwadon abunda mutum ya haddace na Qur'ani gwargwadon matsayinsa a Aljannah.
11- Qur'ani shine littafin da Allaah yayi alƙawarin tsare shi.
12- Binciken likitoci ya tabbatar da cewa duk mai yawan karanta Qur'ani dakuma haddaceshi zai kubuta daga mafi yawan manya-manyan cututtuka da É—an adam ke kamuwa dasu.
13- Mai ƙoƙarin koyan Qur'ani amma yana bashi wahala wurin karantawa yana da lada ninki biyu.
14- Ma'abota Qur'ani suna daga cikin masu Æ™ololuwar daraja da matsayi a Aljannah. 
15- Sannan Qur'ani shine kundin duk wani musulmi, domin duk wani abunda ɗan adam ke buƙata na rayuwar duniya da lahira bakidaya akwai su a Qur'ani.
16- Idan mutum ya karantar da wani Qur'ani to duk ladan da wannan mutumin ya samu shima Allaah zai bashi irin sa.
17- Ma'abocin Qur'ani koyaushe yana cikin kariya na Allaah da mala'ikunsa.
18- Duk makarancin Qur'ani kuma mai aiki dashi mazauninsa na karshe shine ALJANNAH.

Amma ɗan'uwa musulmi duk waɗannan falala da darajoji ba zaka same su ba sai idan ka karanta Qur'ani yadda Allaah ya saukar dashi kuma yadda Manzon Allaah SAW Ya karantar, tareda nisantar duk wasu bid'o'i da aka ƙirƙira wurin karantashi, sannan kuma babban abu kuma shine sai kayi dan Allaah kuma ka yi aiki dashi.

Ga mai son karin bayani game da abubuwan da aka ambata dama wadanda ba a samu damar ambata ba da ganin nassoshin kan haka; zai iya duba waÉ—annan littafan:
1- Al'itqaan na Al-Allaamatus SuyuuÉ—iy.
2- Sahihul Jami'i Na Albaaniy.
3- Al- Musnad na Al- Imam Ahmad.
4- Al- Mu'jam na 'Dabraaniy
2- Da alkutubus sittah.
A karkashin topics na abubuwan da aka ambata.

ALLAH YA SANYAMU CIKIN MA'ABOTA QUR'ANI.

Abdullahi Almadeeniy Kagarko.
30th October, 2015.
Post a Comment (0)