GOMAN ƘARSHE NA RAMADAN

G O M A N K A R S H E

Wadannan kwanaki goma da zamu shiga daga Yau da daddare, suna da matukar muhimmanci a garemu. Domin a cikinsu ne dare mai albarka dare mai falala wato Lailatul Qadar yake.

LAILATUL QADAR Dare ne da ya yafi watanni dubu (1000) albarka. Kuma ana iya yin dace da shi a wadannan kwanaki na karshe.

Yana da kyau Yan uwa mu tashi da karfin mu da jikinmu, mu ajjiye lalaci da kasala mu kara zabura wajan bautar Sarki Allah, domin samun dacewa da rahmar da yake rabawa.

Manzon Allah SAW) Yace:
"Duk wanda ya yi tsayuwar daren Lailatul Qadar yana mai imani da neman lada, an gafarta masa abin daya gabata na zunubansa"
(Bukhari da Muslim)

Lallai akwai ASARA ga musulmin da ya bari kwanakin goman nan suka wuce bai ninka ayyukansa ba. 

Manzon Allah (SAW)
Yana tashin iyalansa domin suyi harama suyi ibada kuma su sami albarka, muyi himma da kara ayyukan alkairi, salloli, karatun Alukr’ani, kyauta, sadaka, zikiri, da addu’o’i. 

Ummahat al-Mu'minin
Nana Aisha; (RA) Tace:
"Ya Manzon Allah! Idan na samu tsayuwar Lailatul Qadr, me zan ce a cikinta? 
ANNABI (SAW) Yace: Kice: “Allahumma innaka ‘afuwwun tuhibbul ‘afwa fa’fu annee"

Ya Allah ka datar da mu a cikin wadannan kwanaki masu albarka, Allah kai ne mai afuwa ka yi mana afuwa, ka gafarta mana da iyayenmu da dukkan musulmi baki daya. Amin.

Barkanmu da shan ruwa 
#sisters & #brothers
#Haruna Saleh


Post a Comment (0)